2019: Idan na zama Gwamnan Kuros Riba, zan kara albashi – John Enoh

2019: Idan na zama Gwamnan Kuros Riba, zan kara albashi – John Enoh

‘Dan takarar gwamnan jihar Kuros Riba a karkashin jam’iyyar APC, John Owan Enoh, ya bayyana cewa zai biya sabon karin albashin da ‘yan kwadago su ke nema na akalla N30, 000 idan ya zama gwamna.

2019: Idan na zama Gwamnan Kuros Riba, zan kara albashi – John Enoh

Sanata John Enoh yace Ayade ya dauki hayar Hadimai har 5000
Source: Depositphotos

Sanata John Enoh wanda yake harin kujerar gwamnan Kuros Riba a APC ya tabbatar mana da cewa gwamnatin sa za ta biya karin albashin ma’aikata idan aka yi dace ya lashe zaben gwamnan jihar da za ayi a cikin watan gobe.

John Enoh ya sha alwashin fara biyan N30, 000 a matsayin mafi karancin albashi a jihar Kuros Riba daga watan Mayun 2019, idan har jam’iyyar APC ce ta samu nasara a zaben Kuros Ribas. Enoh yayi wannan bayani ne jiya.

‘Dan takaran gwamnan na jam’iyyar APC ya gana da ‘yan jarida a Garin Kalaba inda ya bayyana manufar sa. Sanata John Enoh yace yana zama gwamna, zai soke manyan ayyukan da gwamnatin PDP ta a faro domin jihar ta samu kudi.

KU KARANTA: Tsohon Gwamna Fayose ya bayyana shirin murde zabe a 2019

Bayan nan kuma ‘dan takarar yace zai rage adadin Hadimai da mukarraban da aka nada a lokacin gwamna Ben Ayade. John Enoh yace gwamna mai-ci yana barnar dukiyar kasa bayan da ya dauki masu ba shi shawara fiye da 5000.

‘Dan takarar nan APC yace zai adana makudan kudi idan ya soke ayyukan da aka fara a jihar tare da kuma zaftare yawan mukarraban gwamna. Enoh yace muddin yayi wannan, zai samu rarar kudin da zai biya ma’aikata albashi.

‘Yan kwadago su na neman a kara albashi a Najeriya, inda ‘dan takaran na gwamnan Kuros Riba yace hakan ba zai gagara ba, amma tukuna zai tsaya ya duba halin da aka jefa jihar tare da toshe duk wata kafa ta satar kudin gwamnati.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Source: Legit

Mailfire view pixel