Ba ke kadai ba ce Kwamishina a don haka ki ajiye mukamin ki – Fayose ya fadawa Zakari

Ba ke kadai ba ce Kwamishina a don haka ki ajiye mukamin ki – Fayose ya fadawa Zakari

Ayodele Fayose, ya tofa albarkacin bakin sa game da ce-ce-ku-cen da ake tayi game da nada Amina Zakari da aka yi a matsayin babbar jami’ar INEC da za ta sanar da sakamakon zaben 2019.

Ba ke kadai ba ce Kwamishina a don haka ki ajiye mukamin ki – Fayose ya fadawa Zakari

Nadin Amina Zakari ya tsayawa Buhari a wuya – inji Fayose
Source: Depositphotos

Ayodele Fayose ya bayyana cewa an daurawa shugaban kasa Muhammadu Buhari wani nauyi a sakamakon surutun da jama’a su ke yi. Tsohon gwamnan na PDP yace nadin Zakari ya nuna irin mugun shirin da INEC ta ke yi.

Fayose, a cewar sa, nada Hajiya Amina Zakari ta zama Ala-ka-kai a wuyan gwamnatin Buhari tun bayan da aka nada ta wannan mukami. Tsohon gwamnan na Ekiti yayi wannan jawabi ne ta bakin hadimin sa watau Lere Olayinka.

Babban ‘dan adawan kasar yayi watsi da martanin da fadar shugaban kasa ta maida a game da wannan batu, na cewa gwamnatin Goodluck Jonathan ne ta fara nada Amina Zakari a matsayin kwamishinar harkar zabe na INEC.

KU KARANTA: Buhari ya sha alwashin karbe Kwara daga hannun barayi a 2019

Ayo Fayose yace a lokacin da aka nada Zakari a matsayin kwamishina, ba ta da alaka da shugaban kasa mai-ci. Inda ya kara da cewa, asali ma a lokacin, Buhari yayi alkawarin cewa ba zai sake fitowa takarar shugaban kasa ba.

Mista Fayose yace wannan matsayi da aka ba Amina Zakari a 2011, yana cikin irin adalcin gwamnatin PDP da ta shude na. Sai dai yanzu ya nemi ta ajiye mukamin da aka ba ta saboda gudun kar ayi amfani da ita wajen murde zaben bana.

Tsohon gwamnan na PDP ya nemi Zakari ta ajiye wannan nauyi da aka ba ta. Ya kuma ce babu mamaki a karawa IGP wa’adi saboda a murde zaben, yana mai cewa nada Attahiru Jega da aka yi a INEC, shi yasa Buhari ya zama shugaban kasa. .

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel