Siyasar Kano: Zaben jin ra'ayin jama'a ya bayyana wanda zai lashe zaben gwamna

Siyasar Kano: Zaben jin ra'ayin jama'a ya bayyana wanda zai lashe zaben gwamna

Wata kungiya (Poll 4 Excellence Africa (P4EA) ), mai cibiya a kasar Ghana, data kware wajen gudanar da zaben jin ra'ayin jama'a ta fitar da sakamakon zaben jin ra'ayin jama'a da ta gudanar a kan 'yan takarar gwamna a jihar Kano.

A sakamakon da P4EA ta fitar ya nuna cewar gwamnan Kano, Dakta Abdullahi Umar Ganduje, zai lashe zaben gwamna a jihar da kaso 80% na kuri'u da za a kada a zaben watan Fabrairu mai zuwa.

P4EA ta ce gwamna Ganduje na da damar lashe zaben gwamnan jihar Kano da rinjaye mai yawa.

A takardar da kungiyar ta aikewa Ganduje daga ofishinta dake Accra, kasar Ghana, shugaban kungiyar P4EA, Mista Ephraim Nonso, ya taya Ganduje samun nasara a zaben jin ra'ayin da ya dauki tsawon watanni kafin a kammala shi.

Siyasar Kano: Zaben jin ra'ayin jama'a ya bayyana wanda zai lashe zaben gwamna

Ganduje
Source: Depositphotos

A cewar takardar, "muna taya gwamna Ganduje samun wannan gagarumar nasara a zaben jin ra'ayin jama'ar jihar Kano da muka gudanar. Muna gudanar da irin wannan zabe a muhimman jihohin Najeriya 3, kuma nan bada dadewa zamu fitar da sakamakonsu.

DUBA WANNAN: Ba zan kara yin takara ba a rayuwata - Tsohon gwamnan PDP

"Siyasar jihar Kano na daga cikin siyasa mafi jan hankali a Najeriya, hakan ne ma ya saka mu gudanar da zaben jin ra'ayin jama'a a jihar. Mutanen jihar Kano sun nuna matukar gamsuwa da kokarin gwamna Ganduje a bangarori daban-daban."

Takardar ta bayyana cewar daga cikin abubuwan da suka kara wa Ganduje damar lashe zaben gwamnan jihar Kano akwai komawar tsohon gwamnan Kano, Ibrahim Shekarau, jam'iyyar APC da kuma dan takarar gwamna da tsagin Kwankwasiyya suka tsayar.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=ng.legit.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel