Kwamandan Boko Haram ya fadi gari da malamin da ya saka shi a kungiyar

Kwamandan Boko Haram ya fadi gari da malamin da ya saka shi a kungiyar

- Umar Abdulmalik, kwamanda a kungiyar Boko Haram ya bayyana yadda wani Mallam Mustapha ya shigar da shi kungiyar Boko Haram a garin Okene kuma ya koya masa kai hare-hare

- Jami'an 'yan sandan BRT ne suka yi nasarar damke wani kwamandan wanda ke da hannu a tashin bam din Nyanya da wasu hare-hare da dama

- Abdulmalik yana daya daga cikin wadanda suka kai hari a gidan yari na jihar Kogi inda suka kwato wasu 'yan Boko Haram da ke gidan yarin

Wani dan kungiyar Boko Haram, Umar Abdulmalik da jami'an 'yan sanda na IRT suka damke ya bayyana dalla-dalla yadda kungiyar ta shirya tayar da bam din da ya tashi a Nyanya a shekarar 2014 da kuma harin da aka kai a gidan yarin jihar Kogi inda ake tsare da wasu 'yan kungiyar.

A cewar 'yan sanda an kama Abdulmalik ne a ranar Alhamis da ta gabata a gidan 'yar uwarsa da ke unguwar Igando na jihar Legas inda ya tafi jinyar raunin da ake yi masa da harsashi kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

A yayin da ya ke amsa tambayoyin da 'yan sanda su kayi masa, Abdulmalik ya ce bama-baman da akayi amfani da su a Nyanya da hannu aka kera su a jihar Kogi.

Ya kuma fadawa 'yan sanda yadda ya jagoranci wasu 'yan kungiyar kai hare-hare a bankuna da fashi da makami da kashe-kashen mutane a Abuja, Owo a jihar Ondo da Lokoja a jihar Kogi.

Kwamandan Boko Haram ya fadi gari da malamin da ya saka shi a kungiyar

Umar da abokansa
Source: Facebook

Abdulmalik ya shaidawa 'yan sandan cewa ya kashe a kalla mutane 200 kafin a kama shi. Ya ce wani Mallam Mustapha da suka hadu a 2009 ne ya shigar da shi kungiyar ta Boko Haram.

"Na shiga kungiyar Boko Haram ne a Okene karkashin jagorancin wani Zeedi kuma mun tayar da bama-bamai a Kaduna, Kano da Abuja. Zeedi ne ke samar da bama-baman ni kuma aiki na shine kai bama-baman wuraren da muke niyyar kai hari. Bayan wani lokaci, DSS sun gano kungiyar mu inda suka fara kama mambobin mu har da Mallam Mustapha kuma daga baya aka rushe masallacin sa.

"Mun yanke shawarar fara fashin bankuna ne lokacin da kudaden mu suka kare. Zeedi ya kawo mana bindigu kuma ya ce mu kai hari gidan yarin Okene domin mu ceto 'yan uwan mu. Munyi nasara a harin da muka kai kuma daga bisani mukayi fashi a wasu bankuna a Okene.

DUBA WANNAN: Kisan Janar Alkali da Badeh: Akwai lauje a cikin nadi - Rahoton kungiyar Amurka

"Daga baya mun koma garin Owo inda muka sake yiwa wasu bankuna fashi inda muka samu karin kudi na sayan makamai na hada bama-bamai amma daga baya an kama Zeedi da wasu mambobin mu.

"Haka yasa muka tafi Abuja tare da bama-baman da muka kera muka kafa sabuwar kungiya a shekarar 2014 kuma muka kai hare-hare ciki har da na Banex Plaza da Nyanya da Kuje da wasu wurare amma daga baya asirin mu ya tonu kuma an kwace sauran bama-baman mu.

"Nayi sa'a ba a kama ni ba sai na tsere zuwa Kano na buya na tsawon shekaru biyu sannan daga baya na dawo Abuja na hada sabuwar kungiyar fashi da makami." inji shi.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=ng.legit.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel