Badakalar $16bn na wutar lantarki: Shehu Sani ya yiwa APC raddi a kan tuhumar Obasanjo

Badakalar $16bn na wutar lantarki: Shehu Sani ya yiwa APC raddi a kan tuhumar Obasanjo

- Sanata Shehu Sani ya yiwa jam'iyyar APC mai mulki hannun ka mai sanda a kan barazanar da ta keyi na bincikar tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo game da kudin lantarki

- Sanatan mai wakiltan Kaduna ta tsakiya ya ce muddin aka fara binciken za a gano wayoyin lantarki da transiforma na sata a gidajen wasu da ake yiwa kallon salihai a APC

- Sanatan na nufin cewa dai idan ma an sace kudaden ne toh akwai hannun 'yan jam'iyyar APC cikin satar

Sanata Shehu Sani mai wakiltan Kaduna ta tsakiya a majalisar dattawa ya ce akwai mambobin jam'iyyar APC da za su kwan-ciki idan jam'iyyar ta ce za ta binciki tsohon shugaban kasa, Olusegun Obasanjo kan yadda ya kashe $16 biliyan domin gyaran wutan lantarki.

A Mayun shekarar 2018, hukumar yaki da masu yiwa arzikin kasa ta'annati EFCC ta kaddamar da bincike a kan yadda aka kashe Dallan Amurka Miliyan 16 a kan ayyukan gyarar wutan lantarkin karkashin gwamnatin Obasanjo.

Binciken kudin lantarki: Shehu Sani ya yiwa APC kaca-kaca

Binciken kudin lantarki: Shehu Sani ya yiwa APC kaca-kaca
Source: Twitter

DUBA WANNAN: 'Yan ta'addan sun kwace iko da kananan hukumomi 8 a jihar Katsina

A yayin da ya ke mayar da martani, Obasanjo ya ce a shirye ya ke idan ana son a bincike shi bayan shugaba Muhammadu Buhari ya yi zargin an banatar da kudaden da aka ware domin gyarar lantarkin a zamanin Obasanjo.

A wani sako da ya fitar a shafinsa na Twitter, dan majalisar ya ce, "Jam'iyyar APC za ta binciki Baba Obasanjo a kan $16 biliyan na kudin lantarki kamar yadda suke ta barazana, za su gano wayoyin lantarki da transiforma na sata a gidajen wasu 'yan jam'iyyarsu da ake yiwa kallon waliyai."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel