Gwamnatin jihar Kaduna ta samar da kudaden shiga na N30bn a shekarar 2018

Gwamnatin jihar Kaduna ta samar da kudaden shiga na N30bn a shekarar 2018

- Cibiyar tattara haraji da kudaden shiga ta jihar Kaduna ta samar da Naira biliyan 30 a shekarar bara

- Gwamnatin jihar ba ta cimma manufar da kudirta ba na samar da Naira biliyan 42 a bara

- Shugaban cibiyar KDIRS, Mukhtar Ahmed, ya ce gwamnatin ta yi wannan kwazo ne a sakamakon asusun gwamnati na bai daya da ta karba hannu biyu-biyu

Cibiyar tattara kudaden shiga da haraji ta jihar Kaduna, a jiya Juma'a ta bayyana cewa, ta samar da kudaden shiga na Naira biliyan 30 tsakanin watan Janairu zuwa Dasumba na shekarar 2018 da ta gabata kamar yadda jaridar Premium Times ta ruwaito.

Mukhtar Ahmed, shugaban cibiyar ta Kaduna State Internal Revenue Service (KDIRS), shine ya bayar da shaidar hakan yayin ganawa da manema labarai a ranar Alhamis din da ta gabata cikin birnin Kaduna.

Gwamnatin jihar Kaduna ta samar da kudaden shiga na N30bn a shekarar 2018

Gwamnatin jihar Kaduna ta samar da kudaden shiga na N30bn a shekarar 2018
Source: Depositphotos

Mista Ahmed ya bayyana cewa, an samu hauhawa ta kimanin kaso 145 bisa 100 doriya akan kudaden haraji da gwamnatin jihar ta samar tsakanin shekarar 2015 zuwa 2018.

Kamfanin dillancin labarai na Najeriya ya ruwaito cewa, gwamnatin jihar Kaduna ba ta cimma burinta na samar da Naira biliyan 42 da ta kudirta a shekarar 2018, inda ta samu nasarar samar da Naira biliyan 30 kacal a shekarar bara.

KARANTA KUMA: Buhari Uban gida na a gare ni - Gwamna Lalong

Jaridar Legit.ng ta fahimci cewa, gwamnatin jihar ta samu nasarar wannan kyakkyawan kwazo da kuma bajinta a sakamakon asusun gwamnati na bai daya da ta karɓa hannu biyu-biyu tare da dabbaka shi cikin harkokin ta na gudanarwa.

Cikin wani rahoton mai nasaba da wannan, wakilin shiyyar Kaduna ta Tsakiya a majalisar dattawa, Sanata Shehu Sani, ya zargi uwargidan gwamnan jihar Kaduna Mallam Nasir El-Rufa'i, da yada kalaman nuna kiyayya akan sa.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da Shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo cikin shafukan mu na zaurukan sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Source: Legit

Mailfire view pixel