Zabe: Ganduje ya yiwa Aisha albishir mai dadi yayin kamfen din Buhari a Kano, hotuna

Zabe: Ganduje ya yiwa Aisha albishir mai dadi yayin kamfen din Buhari a Kano, hotuna

- A makon da ya gabata ne shugaba Buhari ya rantsar da kwamitin kamfen guda biyu karkashin jagorancin Aisha da Dolapo

- Aisha Buhari zata jagoranci kwamitin yakin neman zabe bangare mata yayin da Dolapo Osinbajo zata jagoranci na matasa

- A yau, Asabar, ne Aisha Buhari ta ziyarci jihar Kano domin kaddamar da yakin neman zaben Buhari a karkashin kwamitin da take jagoranta

Aisha Buhari, uwargidan shugaban kasa Muhammadu Buhari ta kaddamar da yakin neman zaben mijinta na rukunin mata da matasa a jihar Kano.

Da take magana a wurin kaddamar da yakin neman zaben a filin wasa na Sani Abacha dake Kano, Aisha ta nuna karfin gwuiwar cewar mijinta zai lashe zaben 2019.

Ta ce ta shiga sahun masu yiwa APC kamfen a shekarar 2015 saboda kyawawan manufofi da jam'iyyar keda su.

Ziyarar Aisha a Kano: Buhari zai samu fiye da kuri'un da ya samu a 2015 - Ganduje

Ziyarar Aisha a Kano
Source: Facebook

Ziyarar Aisha a Kano: Buhari zai samu fiye da kuri'un da ya samu a 2015 - Ganduje

Ziyarar Aisha a Kano
Source: Facebook

Ziyarar Aisha a Kano: Buhari zai samu fiye da kuri'un da ya samu a 2015 - Ganduje

Ziyarar Aisha a Kano
Source: Facebook

Ziyarar Aisha a Kano: Buhari zai samu fiye da kuri'un da ya samu a 2015 - Ganduje

Ziyarar Aisha a Kano
Source: Facebook

A cewar ta, "yanzu gwamnatin tarayya ta kaddamar da duk manufofin da jam'iyyar APC ta zo da su a karkashin ofishin mataimakin shugaban kasa."

"Mijina ya lashe zaben shekarar 2015 ba tare da bawa 'yan Najeriya ko sisi ba, saboda haka, yanzu haka ma zai lashe zaben ranar 16 ga watan Fabrairu."

DUBA WANNAN: Ba zan kara yin takara ba a rayuwata - Tsohon gwamnan PDP

A nasa bangaren, Dakta Abdullahi Umar Ganduje, gwamnan jihar Kano, ya ce Buhari zai samu kuri'u fiye da wadanda ya samu a zaben shekarar 2015.

Ganduje ya bayyana cewar gwamnatin APC ta shimfidawa jama'a aiyukan alheri tare da bayyana cewar jama'a zasu zazzaga mata kuri'u a zabe mai zuwa.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=ng.legit.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel