Buhari Uban gida na a gare ni - Gwamna Lalong

Buhari Uban gida na a gare ni - Gwamna Lalong

- Kasancewar Buhari Uban gida ne a gare ni ba bu wani dalili da zai sanya na gaza bayar da raina domin shi inji gwamnan jihar Filato, Simon Lalong

- Shugaban jam'iyyar APC Kwamared Adams Oshiomhole ya yi kira kan zaben dukkanin 'yan takara da ke karkashin inuwa ta jam'iyyar APC

- Gwamnatin jam'iyyar APC za ta tabbatar da fidda talakawan kasar nan daga kangi na talauci inji Ministan sufuri Rotimi Amaechi

Shugaban jam'iyyar APC na kasa, Kwamared Adams Oshiomhole, ya sake busa sarewarsa ta kiran al'ummar Najeriya wajen zaben dukkanin 'yan takara a kowane mataki da ke karkashin inuwa ta jam'iyyar APC domin tabbatar da fidda kasar nan zuwa ga tudun tsira.

Kazalika gwamnan jihar Filato, Simon Bako Lalong, ya yi makamancin wannan kira da cewar ba bu shakka zaben dukkanin 'yan takara da ke karkashin inuwa ta jam'iyyar APC a kowane mataki zai tabbatar da kai kasar nan zuwa gaci.

Buhari Uban gida na a gare ni - Gwamna Lalong

Buhari Uban gida na a gare ni - Gwamna Lalong
Source: UGC

Kamar yadda majiyar jaridar Legit.ng ta ruwaito, Rotimi Amaechi, shugaban kungiyar yakin neman zaben shugaban kasa Buhari, shima ba a barshi a baya ba wajen wannan kira da cewar zaben jam'iyyar APC zai yi tasirin gaske wajen fidda talakawan kasar nan daga kangi na talauci.

Dukkanin su sun yi wannan kira ne yayin kaddamar da yakin neman zaben shugaban kasa Muhammadu Buhari da kuma gwamnan jihar Filato Lalong da aka gudanar a jihar sa.

KARANTA KUMA: Za mu koma Teburin sulhu da kungiyar ASUU a ranar Litinin - Ngige

Gwamna Lalong wanda ya gabatar da takaitattun jawabai yayin gangami na taron ya bayyana cewa, shugaban kasa Buhari ya kasance Uban gida a gare sa da ko shakka ba bu zai iya bayar da ransa a gare sa.

Cikin wani rahoton mai nasaba da wannan, jaridar Legit.ng ta ruwaito cewa, an ji Ministan sufuri, Rotimi Amaechi, ya na caccakar shugaban kasa Buhari da cewa ba ya ji ballantana sauraron shawarar kowa cikin wani faifan sautin murya.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da Shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo cikin shafukan mu na zaurukan sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Source: Legit Nigeria

Mailfire view pixel