Sanata Sani ya gargadi magoya bayan APC kan yi wa Buhari da sauransu kamfen din gida-gida

Sanata Sani ya gargadi magoya bayan APC kan yi wa Buhari da sauransu kamfen din gida-gida

Sanata Shehu Sani ya gargadi magoya bayan jam’iyyar All Progressives Congress (APC) da aka dauka aikin yiwa Shugaban kasa Muhammadu Buhari da sauran yan takarar jam’yya mai mulki kamfen din gida-gida da su yi taka-tsan-tsan.

Sanatan mai wakiltan yankin Kaduna ta tsakiya kuma dan jam’iyyar Peoples Redemption Party (PRP) ya yi ikirarin cewa magoy bayan za su hadu da fusatattun yan Najeriya da yawa wadanda ba su farin ciki da halin da kasar ke ciki.

Ya gargadi mabiyan jam’iyyar da su lura da kyau sab oda kada fusatattun masu jefa kuri’a su far masu da hari.

Ya bayyana hakan ne a wasu rubutu da ya wallafa a shafinsa na twitter a ranar Juma’a, 4 ga watan Janairu.

KU KARANTA KUMA: 2019: PDP ta fara karfi a wata jihar arewa yayinda yan APC da PDM 4,500 suka koma jam’iyyar

A wani lamari na daban, mun ji cewa Sanata Shehu Sanin ya zargi uwargidan gwamnan jihar Kaduna da yada kalaman kiyayya akan shi.

A wani rubutu da ya wallafa a shafukansa na Facebook da Twitter a ranar Asabar, 5 ga watan Janairu, sanatan mai wakiltan Kaduna ta tsakiya ya bukaci Gwamna Nasir El-Rufai da ya gargadi matarsa kan wanzar da lamuran kamfen dinta akan gashin kansa a koda yaushe.

Sanatan yace yana kallon wannan aiki na uwargidan gwamnan a matsayin wani hari akan shi da kuma kalaman kiyayya. Ya yi gargadin cewa idan gwamnan bai daidaita uwargidan tasa ba, zai kai kararta wajen hukumomin addini a jihar.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=ng.legit.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel