Ba zan kara yin takara ba a rayuwata - Tsohon gwamnan PDP

Ba zan kara yin takara ba a rayuwata - Tsohon gwamnan PDP

Tsohon Sanata kuma tsohon gwamnan jihar Oyo, Rashidi Ladoja, ya ce ya yi ritaya daga yin takarar kowacce kujera a Najeriya saboda wahalar da ya ce ya sha lokacin da yake gwamna.

Ladoja, mai rike da mukamin Olubadan na kasar Ibadan, ya zama gwamna a jihar Oyo a tsakanin shekarar 2003 zuwa shekarar 2007 a karkashin jam'iyyar PDP. An tsige shi a watan Janairu na shekarar 2006, amma kotu ta mayar da shi a watan Disamba na shekarar.

Da yake wannan kalami a yau, Asabar, Ladoja ya bayyana cewar ya yanke shawarar yin bankwana da takara ne saboda samun lokacin kulawa da bukatun iyalinsa.

A hirar sa da manema labarai a garin Igholo, hedkwatar karamar hukumar Oorelope, Ladoja ya ce, "kadan ya rage na manta da iyalina lokacin da nake gwamnati. Mun yi iya bakin kokarinmu, amma ni kam ba zan kara yin takara ba."

Ba zan kara yin takara ba a rayuwata - Tsohon gwamnan PDP

Sanata Rashidi Ladoja
Source: Depositphotos

A baya Legit.ng ta kawo maku labarin cewar Buba Galadima, kakakin kwamitin yakin neman zaben dan takarar shugaban kasa a karkashin jam'iyyar PDP, Atiku Abubakar, ya bawa jama'a mamaki bayan ya bayyana a wani shirin gidan talabijin din Arise TV sanye da rigar jam'iyyar APC domin yiwa Atiku kamfen.

Galadima ya bayyana a gidan talabijin din ne domin kare manufofin jam'iyyar PDP da dan takarar ta na shugaban kasa, Atiku Abubakar.

DUBA WANNAN: 2019: Tsohon shugaban jam'iyyar PDP ya koma

A kwanakin baya bayan nan ne Galadima ya furta cewar a halin da Najeriya ke ciki a yanzu, tamkar Buhari ya mika mulki ga Atiku ne.

Sai dai ganinsa cikin rigar APC ya bawa jama'a mamaki tare da jawo barkewar cece-kuce a kan manufar sa ta zuwa gidan talabijin domin kare gwaninsa da jam'iyyar sa amma sanye da rigar jam'iyyar APC mai mulki.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=ng.legit.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel