Katobara! An jiyo Amaechi na caccakar Buhari, bai so hakan ta fallasa ba

Katobara! An jiyo Amaechi na caccakar Buhari, bai so hakan ta fallasa ba

- An saki wani sautin muryar Amaechi na kalubalantar Buhari

- Anyi barazanar sakin sauran sautikan matukar ya karata

- Har yanzu Amaechi bai maida martani ba don mai magana da yawun shi yaki daukar kiran

Katobara! An jiyo Amaechi na caccakar Buhari, bai so hakan ta fallasa ba

Katobara! An jiyo Amaechi na caccakar Buhari, bai so hakan ta fallasa ba
Source: Depositphotos

Darakta Janar na kungiyar yakin neman zaben shugaban kasa Muhammadu Buhari, Rotimi Amaechi, ana zargin shi da kalubalantar shugaban kasa Muhammadu Buhari.

Tsohon mataimaki na musamman ga tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan, Reno Omokiri ne ya sanyan amon sautin a shafin shi na tuwita.

A sautin wanda ba a tabbatar da ingancin shi ba, Amaechi wanda shine ministan sufuri ya bayyana cewa Buhari baya karanta komai kuma baya sauraren kowa.

An ruwaito Amaechi yace, "Shugaban kasa baya sauraren kowa. Bai damu ba. Ka rubuta komai da kake so. Shugaban kasa bai damu ba. Yana karatu ne?

Amma wanda ministan ke fadawa hakan ba a sanar ba.

DUBA

WANNAN: Ya kurmantar dani, sannan ya binne danmu ba da sani na ba, mace ta fada wa kotu

Omokri wanda dan gani kashe nin kalubalantar gwamnatin Buhari, yace yana da shaidu da zai nuna ingancin sautin.

Yayi barazanar sakin wasu sautikan matukar Amaechi ya musa ingancin wannan.

Omokri ya rubuta, "Muna da sautikan Chibuike Amaechi, inda yake fadin munanan abubuwa akan gwamnatin Buhari. Naji Amaechi yana so yace da Goodluck Jonathan yake. Yace hakan ni kuma zan saki na biyun wanda zai nuna kiri kiri da Buhari yake."

Omokri yace Amaechi baya mutunta Buhari kuma ya fadi a wani sautin muryar shi da aka dauka cewa tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo ne kadai shugaban da yake mutuntawa.

Yunkurin samun martani daga Amaechi ya tashi a banza saboda mai magana da yawun shi, David Iyofor baya daukar waya ko sakon kar ta kwana da aka tura mishi ranar asabar.

Shafin NAIJ.com Hausa ne ya koma LEGIT.ng Hausa

Latsa kuga sabuwar manhajar Legit.ng Hausa a wayarku ta salula: https://play.google.com/store/apps/details?id=ng.legit.hausa&hl=en

Shafukanmu na dandalin sada zumunta sune:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel