Abun boye ya fito fili: An ji Amaechi na caccakar Buhari a wani faifan sautin murya

Abun boye ya fito fili: An ji Amaechi na caccakar Buhari a wani faifan sautin murya

Tsohon hadimin tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan ya saki wani faifan sautin murya a shafinsa na Tuwita dake bayyana Rotimi Amaechi, babban darektan yakin neman zaben shugaba Buhari na sukar shugaban kasar.

A cikin faifan sautin muryar mai tsawon kasa da dakika 10, Omokri ya ce sautin muryar Amaechi ne yayin da yake sukar Buhari.

A cikin sautin muryar da majiyar mu bata iya tantance ko muryar waye ba, an ji mai magana a ciki na cewa shugaba Buhari ba ya ji ko sauraron shawarar kowa.

Abun boye ya fito fili: An ji Amaechi na caccakar Buhari a wani faifan sautin murya

Abun boye ya fito fili: An ji Amaechi na caccakar Buhari a wani faifan sautin murya
Source: Depositphotos

DUBA WANNAN: 'Yan ta'addan sun kwace iko da kananan hukumomi 8 a jihar Katsina

"Shugaban kasa baya sauraron kowa kuma bai damu ba. Ba ya karanta duk abinda aka aika masa a rubuce," a faifan sautin muryar da ake zargin na Amaechi ne.

Omokri ya rubuta cewar, "muna da cikakken sautin muryar Amaechi da aka nada a sirrance yana furta kalamai marasa dadi a kan gwamnatin Buhari duk da yana kokarin wayancewa wai yana magana ne a kan Jonathan.

"Idan ya kara alakanta kalaman da ya yi da Jonathan zan saki wani sautin muryar."

Omokri ya zargi Amaechi da nuna raini ga Buhari tare da bayyana cewar a wani sautin muryar Amaechi ya ce tsohon shugaban kasa Obasanjo kadai yake girmamawa.

Kokarin jin ta bakin David Iyofor, kakakin Amaechi a kan wannan batu bai samu ba.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel