Kuskure ne mika Najeriya hannun Atiku - Na hannun damar Buhari

Kuskure ne mika Najeriya hannun Atiku - Na hannun damar Buhari

- Jagoran kungiyar wayar da kan magoya bayan Buhari, Kailani Muhammad ya ce kuskure ne damkawa tattalin arzikin Najeriya a hannun Atiku

- Kailani Muhammadu ya lissafo laifukan da kwamitocin bincike da dama suka ambacci suna Atiku musamman daga shekarun 1999 zuwa 2007

- Kailani ya ce Shugaba Muhammadu Buhari ya taka rawar gani cikin shekaru uku da rabi da ya yi kan mulki saboda haka ya yi kira da al'umma su zabe shi a 2019

Na hannun daman Shugaba Muhammadu Buhari kuma jagoran Buhari Awareness and Voters' Guard, Injiniya Kailani Muhammad ya ce tsohon mataimakin shugaban kasa kuma dan takarar shugabancin kasa na PDP, Atiku Abubakar bai cancanci a damka masa amanan 'yan Najeriya ba.

Ya ce akasin Shugaba Muhammadu Buhari, Atiku yana da zargin rashawa da suka dabaibaye shi wadda ya gaza warwarewa.

Jigon na jam'iyyar All Progressives Congress (APC), ya ce ba dai-dai bane a damka tattalin arzikin Najeriya a hannun Atiku a yayin hirar sa da manema labarai a Kaduna.

Kuskure ne mika Najeriya hannun Atiku - Na hannun damar Buhari

Kuskure ne mika Najeriya hannun Atiku - Na hannun damar Buhari
Source: UGC

DUBA WANNAN: Tashin hankali: Wani mutum ya cinna wa kansa wuta saboda matar sa tayi yaji

A cewar jigon na jam'iyyar APC, "A yayin da mafi yawancin 'yan Najeriya sunyi na'am da Buhari a matsayin mutum mai gaskiya da nagarta, mutane da yawa basu amince da Atiku ba saboda zargin rashawa da cin hanci da aka dade ana masa."

A yayin da ya ke lissafo nasarorin da Shugaba Buhari ya samu, ya ce, "a cikin shekaru 3 da rabi da aka shugaba Buhari ya yi mulki, ya gina manyan-manyan tituna guda 25 da duka yankunan siyasa 6 na Najeriya ta hanyar N100 biliyan na Sukuk a 2017.

"Saboda hangen nesan sa, layyukan dogo sun fara aiki. Cikin kankanin lokaci aikin wutan lantarki na Mambilla zai kammalu. Shirin bawa manoma bashi ya sanya kananan manoma da yawa sun zama miloniyoyi."

A bangaren Atiku kuma, ya ce "an damkawa Atiku kudi domin gyarar wutan lantarki amma kudin sun bace kuma a shekarar 2007 kwamitin majalisar dattawa karkashin jagorancin Ndoma-Egba da EFCC ta samu Atiku da laifin karkatar da $145 miliyan na PTDF zuwa asusun ajiyarsa daga 1999 zuwa 2006."

Ya cigaba da cewa kwamitin bincike na tsohon sufeta janar na 'yan sanda, Mike Okiro da samu Atiku da laifin karbar rashawar $74 miliyan na Halliburton tare da wasu manyan jami'an gwamnati.

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel