Zaben 2019: Atiku ya sake yin kaca-kaca da Buhari kan nade-naden gwamnatin sa

Zaben 2019: Atiku ya sake yin kaca-kaca da Buhari kan nade-naden gwamnatin sa

Dan takarar shugaban kasa karkashin tututar Jam’iyar PDP Alhaji Atiku Abubakar yace babu adalci a yadda Shugaba Muhammadu Buhari na jam'iyyar APC yake raba mukamai a gwamnatin tare da bayar da tabbacin gyara matsalar idan aka zabe shi.

Tsohon mataimakin shugaban kasar na Najeriya, Atiku Abubakar din dai ya bayyana hakan ne a cikin wata hirarshi da yayai da Sashen Hausa na gidan Jaridar Muryar Amurka.

Zaben 2019: Atiku ya sake tika Buhari da kasa a wani zaben gwaji na yanar gizo

Zaben 2019: Atiku ya sake tika Buhari da kasa a wani zaben gwaji na yanar gizo
Source: Facebook

KU KARANTA: Hukumar Kwastam ta kama motar Dangote da haramtattun kaya

Legit.ng Hausa ta samu cewa ya kuma ce rashin adalcin baya rasa nasaba da rikicin kabilanci da addinin da ake fama da su a sassa da dama na kasar wannan lokacin.

Da yake bayyana yadda zai tunkari wannan matsala, Alhaji Atiku yace idan shugaba ya yi adalci ya ba kowanne addini da kuma kowanne bangare hakinshi za a zauna lafiya.

Yace “idan aka dubi shugabancin jami’an tsaron Najeriya gaba daya, kusan wajen mutum ashirin, a cikin wajen mutum ashirin din nan, wata kila mutum daya ne ko biyu daga kudu, sauran duk daga arewa ne, kuma a ce kusan yawancinsu addini guda.

Dan takarar shugaban kasar na jam’iyar PDP ya bayyana cewa, ana fama da yawan tashin hankali ne a arewacin Najeriya domin su ne suke da filayen noma kuma dabbobi a arewa suke.

Ya kuma bayyana cewa matakin farko da zai dauka na shawo kan wannan matsalar idan ya zama shugaban kasa shi ne zaunawa da bangarorin domin fahimtar juna.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma legit.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://web.facebook.com/legitnghausa?_rdc=1&_rdr

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel