Tsaro: Rundunar sojin sama zata bude wata muhimmiyar cibiya a Sokoto

Tsaro: Rundunar sojin sama zata bude wata muhimmiyar cibiya a Sokoto

Shugaban hafsin sojojin saman Najeriya, Air Marshall Sadiqque Abubakar ya ce rundunar sojin sama zata kafa sansanin kai dauki na gaggawa a Sokoto da za su rika taimakawa sojojin da ke atisayen Operation Diramikiya a yankin Arewa maso yamma.

Abubakar ya sanar da hakan ne a yayin da ya ziyarci mukadashin gwamnan jihar Zamfara, Alhaji Sanusi Rikiji a gidan gwamnati a ranar Laraba a Gusau kamar yadda NTA ta ruwaito.

Ya ce ya ziyarci jihar ne domin ya dubba halin da dakarun sojojin NAF ke ciki a yunkurin su na tabbatar da zaman lafiya mai dorewa a yankin.

Tsaro: Rundunar sojin sama zata bude wata muhimmiyar cibiya a Sokoto

Tsaro: Rundunar sojin sama zata bude wata muhimmiyar cibiya a Sokoto
Source: Twitter

DUBA WANNAN: Tashin hankali: Wani mutum ya cinna wa kansa wuta saboda matar sa tayi yaji

Shugaban sojin saman ya yabawa gwamnatin jihar da mazauna jihar bisa goyon bayan da suke bawa hukumomin tsaro da ke yaki da 'yan ta'adda a yankin musamman ta fannin taimaka musu da bayannan sirri.

Abubakar ya umurci al'ummar jihar su cigaba da bawa hukumar sojin hadin kai wurin bayar da bayannan sirri domin hakan yana daga cikin hanyoyin da za a samu nasarar dakile 'yan ta'addan.

Rikiji, wadda shine kuma Kakakin majalisar dokokin jihar ya mika godiyarsa ga Abubakar bisa ziyarar da ya kawo musu inda ya ce hakan ya nuna gwamnatin tarayya tana bayar da muhimmanci kan samar da tsaro a jihar.

Ya bayar da tabbacin cewa gwamnatin jihar za ta cigaba da tallafawa hukumar sojin a dukkan hanyoyin mai yiwuwa domin ganin an samu nasarar kawar da 'yan ta'addan.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel