Jonathan ne ya ba ni mukami ba Buhari ba — Amina Zakari

Jonathan ne ya ba ni mukami ba Buhari ba — Amina Zakari

- Amina Zakari ta musanta zargin cewa tana da dangantaka ta jini da shugaba kasa Muhammadu Buhari

- Ta jadadda cewa an ga ta cancanta tayi aikin ne shiyasa aka bata aikin

- Kwamishinar hukumar zaben ta ce Jonathan ne ya bata aiki ba Buhari ba, domin a cewarta shi kan shi Buhari ya zo ne ya same ta ne kan aikin nan yace ta ci gaba

Kwamishinar hukumar zabe mai zaman kanta (INEC) Amina Zakari ta musanta zargin cewa tana da dangantaka ta jini da shugaba kasa Muhammadu Buhari.

Ta bayyana cewa Daura da Kazaure kusa kusa ne amma bata da dangantaka ta jini da Buhari.

"Ba mu da dangantaka ta jini da shugaban kasa Muhammadu Buhari kuma ko akwai dangantaka ba za ta hana mutum yi wa kasa aiki yadda ya kamata ba."

Jonathan ne ya ba ni mukami ba Buhari ba — Amina Zakari

Jonathan ne ya ba ni mukami ba Buhari ba — Amina Zakari
Source: UGC

Amina ta kara da cewa aikin da aka ba ta ba wai tattara kuri’a bane aikin zai tabbatar inda za a tattara kuri’a kowa da ya shiga zai samu kwanciyar hankali da lumana.

Ta jadadda cewa an ga ta cancanta tayi aikin ne shiyasa aka bata aikin.

Da aka tambayeta cewa wasu na zargin Buhari ya bata aikin nan ne saboda kusancinsu Amina tace : “Jonathan ne ya bani aiki ba Buhari ba, Buhari ya zo ne ya same ni ne kan aikin nan yace in ci gaba. Saboda haka duk wannan hayaniyar da ake yi tunda nayi aiki da su masu hayaniyar sais u fito su nuna inda suka ga nayi wani abu ba daidai ba tun daga 2010 zuwa yau."

KU KARANTA KUMA: Sanata Shehu Sani ya zargi uwargidan Gwamna El-Rufai da kalaman kiyayya

Wasu 'yan siyasar kasan ne dai suka fara zarge-zargen cewa tana da dangantaka da Buhari, don haka suna da shakku kan adalcin da INEC za ta yi a zaben dake tafe.

An nada Amina a matsayin mai kula da tattara sakamako, abinda ya sa 'yan adawar ke ganin za a yi musu magudi.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=ng.legit.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel