Za mu koma Teburin sulhu da kungiyar ASUU a ranar Litinin - Ngige

Za mu koma Teburin sulhu da kungiyar ASUU a ranar Litinin - Ngige

Mun samu cewa gwamnatin tarayyar Najeriya ta kayyade ranar Litinin a matsayin ranar komawa kan teburin sulhu da kungiyar malaman jami'o'in Najeriya ta ASUU, domin neman sasanci kan tayar da kayar baya na yajin aiki da ta afka watanni biyu da suka gabata.

Gwamnatin tarayyar Najeriya ta zayyana cewa, za ta koma kan teburin ta na sulhu da kungiyar malaman jami'o'in Najeriya ta ASUU dangane da yajin aikin malaman jami'o'in kasar nan da ke ci gaba da barin baya da kura.

Ministan kwadago da ayyuka, Sanata Chris Ngige, shine ya bayar da sanarwar hakan cikin wani sako da sa hannu babban sakataren sadarwa na ma'aikatarsa, Mista Samuel Olowookere, a yau Asabar cikin babban birnin kasar nan na tarayya.

Za mu koma Teburin sulhu da kungiyar ASUU a ranar Litinin - Ngige

Za mu koma Teburin sulhu da kungiyar ASUU a ranar Litinin - Ngige
Source: UGC

A cewar rahoton, gwamnatin za ta dora daga matsayarta na ci gaba da neman sulhu da kuma sasanci tsakanin ta da kungiyar malaman jami'o'in kasar nan domin kawo karshen tayar da kayar baya na yajin aiki da ta afka tsawon watanni biyu da suka gabace mu.

Majiyar jaridar Legit.ng ta ruwaito cewa, gwamnatin tarayya ta kayyade karfe 3.30 na Yammacin ranar Litinin 7 ga watan Janairu na wannan shekara domin ci gaba da gudanar da zaman sulhu tsakanin ta da fusatattun malamai.

Kungiyar ASUU ta afka cikin yajin aikin sai mama-ta-gani tun a ranar 5 ga watan Nuwamba na shekarar 2018 da ta gabata sakamakon rashin cika alkawurra da yarjejeniyar da ta kulla da gwamnatin tarayya tun a shekarar 2009.

KARANTA KUMA: 2019: Dan takara mai akida da manufar sauya fasalin kasa za mu zaba - Kabilar Ibo

Kadan daga cikin bukatun da kungiyar ASUU ke neman cikawar su sun hadar da inganta jin dadin malamai da kuma dalibai musamman ta fuskar inganta ci gaban gine-gine da kuma kayan karantarwa na zamani.

Jaridar Legit.ng ta ruwaito cewa, a ranar Alhamis din da gabata shugaban kasa Muhammadu Buhari, ya yi furuci na kyautata zaton sulhuntawa da kungiyar ASUU nan ba da jimawa ba yayin da kungiyar daliban Najeriya ta ziyarci fadarsa ta Villa da ke garin Abuja.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da Shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo cikin shafukan mu na zaurukan sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Source: Legit Newspaper

Mailfire view pixel