2019: Dan takara mai akida da manufar sauya fasalin kasa za mu zaba - Kabilar Ibo

2019: Dan takara mai akida da manufar sauya fasalin kasa za mu zaba - Kabilar Ibo

Da sanadin shafin jaridar Vanguard mun samu rahoton cewa, kungiyar kabilar Ibo ta Igbo World Assembly, IWA, ta yanke shawarar rashin goyin bayan duk wani dan takara maras akida da manufa ta sauya fasali da yiwa Najeriya garambawul.

Jagoran kungiyar, Dakta Nwacukwu Anakwenze, shine ya bayar da wannan sanarwa da cewa kungiyar ba za ta goyi bayan duk wani dan takara da ba bu sauya fasalin kasa cikin akidu da manufofin sa na tsare-tsaren shugabancin kasar nan.

Anakwenze ya yi furucin hakan yayin ganawar sa da manema labarai cikin birnin Awka na jihar Anambra a ranar Juma'ar da ta gabata. Ya ce wannan shawara ta bayu ne sakamakon muhimmancin sauya fasalin kasar nan da ya zamto wani babban tafarki na ci gaba.

2019: Dan takara mai akida da manufar sauya fasalin kasa za mu zaba - Kabilar Ibo

2019: Dan takara mai akida da manufar sauya fasalin kasa za mu zaba - Kabilar Ibo
Source: UGC

A cewar sa, duk wani dan takara da ba ya da akidu na tsare-tsare da manufofin sauya fasalin kasa tare da yi mata garambawul da kuma gididdiba iko na jagoranci, to kuwa ba za ya samu goyon bayan kungiyar su ba.

Ya ci gaba cewa, kungiyar da ta mamaye dukkanin wata al'ada da zamantakewa ta al'ummar kabilar Ibo tana da yakinin cewa, sauya fasalin kasa za ya yi tasirin gaske wajen kawo mafitar kalubalai na habaka da ci gaba da kasar nan ta ke fuskanta a halin yanzu.

KARANTA KUMA: Kotu ta zartar da hukuncin rataya kan wasu 'yan fashi da makami 2 a jihar Ondo

Ya yi zargin yadda rikon sakainar kashin ta fuskar jagoranci na shugabannin kasar nan ta haddasa kalubalai da ake ci gaba da fuskanta a kasar nan kama daga rashin tsaro, cin hanci da rashawa, rashin aikin yi, yunwa, talauci, karancin masana'antu da kuma ta'addanci.

Dakta Anakwenze ya kuma yi kira ga daukacin al'ummar kasar nan akan su fito kwansu da kwarkwata domin yakar duk wani nau'i na magudi ko rashin adalci a yayin babban zaben kasa da za a gudanar watan gobe.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da Shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo cikin shafukan mu na zaurukan sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Source: Legit

Mailfire view pixel