Sanata Shehu Sani ya zargi uwargidan Gwamna El-Rufai da kalaman kiyayya

Sanata Shehu Sani ya zargi uwargidan Gwamna El-Rufai da kalaman kiyayya

- Sanata Shehu Sani ya zargi uwargidan gwamnan jihar Kaduna da yada kalaman kiyayya akan shi

- Sani ya bukaci Gwamna Nasir El-Rufai da ya gargadi matarsa kan wanzar da lamuran kamfen dinta akan gashin kansa a koda yaushe

- Ya kuma caccaki kungiyar makiyayan Najeriya, na Miyetti Allah kan goyon bayan dan uwansu Bafulatani guda a zaben shugaban kasa mai zuwa

Sanata Shehu Sanin a jam’iyyar Peoples Redemption Party (PRP) ya zargi uwargidan gwamnan jihar Kaduna da yada kalaman kiyayya akan shi.

A wani rubutu da ya wallafa a shafukansa na Facebook da Twitter a ranar Asabar, 5 ga watan Janairu, sanatan mai wakiltan Kaduna ta tsakiya ya bukaci Gwamna Nasir El-Rufai da ya gargadi matarsa kan wanzar da lamuran kamfen dinta akan gashin kansa a koda yaushe.

Sanata Shehu Sani ya zargi uwargidan Gwamna REl-Rufai da kalaman kiyayya

Sanata Shehu Sani ya zargi uwargidan Gwamna REl-Rufai da kalaman kiyayya
Source: Twitter

Sanatan yace yana kallon wannan aiki na uwargidan gwamnan a matsayin wani hari akan shi da kuma kalaman kiyayya.

Ya yi gargadn cewa idan gwamnan bai daidaita uwargidan tasa ba, zai kai kararta wajen hukumomin addini a jihar.

A wani rubutu daban da ya wallafa a shafinsa a rtanar Juma’a, 4 ga watan Janairu, sanatan ya caccaki kungiyar makiyayan Najeriya, na Miyetti Allah kan goyon bayan dan uwansu Bafulatani guda a zaben shugaban kasa mai zuwa.

KU KARANTA KUMA: Atiku: Buba Galadima ya bayyana a gidan talabijin da rigar APC

A cewar Sanata Sani, kungiyar ta sanya kanta a wani irin mawuyacin hali, ta hanyar daukar wannan motsi na son kai. A nasa, kungiyar wacce ke wakiltan Fulani kamata yayi ta kasance a tsaka-tsaki cikin lamarin.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=ng.legit.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel