An fara amfani da sunan EFCC ana yaudarar mutane, EFCCn ta dauki sabbin matakai

An fara amfani da sunan EFCC ana yaudarar mutane, EFCCn ta dauki sabbin matakai

- Hukumar nan ta EFCC ta janyo hankalin mutane akan masu yin damfara da sunan ta

- Orilade yace hukumar ta samu sakwanni da dama wanda aka aika da sunan ta

- Yayi kira ga al'umma da karsu sake su turawa wadannan mutane kudi da zummar za'a rufe case din su

Sharuddan Saudiyya ga Najeriya kan hajjin 2019

Sharuddan Saudiyya ga Najeriya kan hajjin 2019
Source: Facebook

Hukumar nan ta EFCC tace yanzu haka ta maida hankalin ta akan wasu yan damfara dake cewa su jami'an hukumar ne inda suke turawa mutane sako suna neman kudi a wajensu.

Tony Orilade mai magana da yawun hukumar ya bayyana haka a jiya a Abuja cewa hukumar su bata taba neman wani abu a hannun wani ba akan za'a kashe case dinsa.

DUBA WANNAN: Ya kurmantar dani, sannan ya binne danmu ba da sani na ba, mace ta fada wa kotu

Orilade ya bayyana cewa hukumar ta samu sakwanni da dama wanda wadannan yan damfara ke amfani dashi.

Daga karshe yayi kira ga al'umma da karsu sake su turawa kowa kudi da sunan hukumar ta EFCC.

An dai saba jin yadda ake zabga yaudara a duniya, inda Najeriya tayi kaurin suna a kasashen duniya, lamari da yasa ake kasa yarda ayi kasuwanci da 'yan Najeriya, fatan gwamnati dai shine martabar ta dawo.

Shafin NAIJ.com Hausa ne ya koma LEGIT.ng Hausa

Latsa kuga sabuwar manhajar Legit.ng Hausa a wayarku ta salula: https://play.google.com/store/apps/details?id=ng.legit.hausa&hl=en

Shafukanmu na dandalin sada zumunta sune:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel