A bana, yansanda zasu fara kama masu satar banten mata da laifin kokarin kisan kai

A bana, yansanda zasu fara kama masu satar banten mata da laifin kokarin kisan kai

- Za a fara yankewa barayin Dan kamfai hukuncin kisa

- Sukanyi amfani da su ne wajen tsafa ce tsaface

- Barayin sun bayyana cewa tsafin na iya halaka mai kayan

A bana, yansanda zasu fara kama masu satar banten mata da laifin kokarin kisan kai

A bana, yansanda zasu fara kama masu satar banten mata da laifin kokarin kisan kai
Source: Depositphotos

Jami'ar hulda da jama'a na yan sandan jihar Legas tace za'a fara hukunta masu satar kayan ciki irinsu singileti, rigar mama da dan kamfai da laifin yunkurin kisa ba wai laifin sata ba.

A watannin da suka gabata, an samu yawon satar kayan ciki wanda ake yadawa cewa suna satar ne don tsafi wanda hakan zai iya kawo ajaliny mai kayan.

An kama wani mutumi a ranar Alhamis a Akure, jihar Ondo, dauke da jaka cike da kayan ciki na mata da kunzugu.

DUBA WANNAN: Wata mata da ta suma tun 2005 ta haihu cikin bacci, ko ta yaya hakan ta faru

Dolapo Badmos, mai magana da yawun yan sandana yanki na 2 ta tabbatar da cewa barayin da ake kamawa da Dan kamfan mata sun bayyana cewa suna amfani da su ne don yin tsafin da zai yi ajalin mai Dan kamfan.

Kamar yanda rahoton ya fada, matsafa na tura yan aike maza da mata wadanda ke taimakon su don samo kayan ciki na maza bayan gama jima'i.

Amma kuma babu wani sashi na kundin tsarin mulkin Najeriya da ya goyi bayan hakan.

Shafin NAIJ.com Hausa ne ya koma LEGIT.ng Hausa

Latsa kuga sabuwar manhajar Legit.ng Hausa a wayarku ta salula: https://play.google.com/store/apps/details?id=ng.legit.hausa&hl=en

Shafukanmu na dandalin sada zumunta sune:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng News

Mailfire view pixel