'Yan ta'addan sun kwace iko da kananan hukumomi 8 a jihar Katsina

'Yan ta'addan sun kwace iko da kananan hukumomi 8 a jihar Katsina

- Gwamnatin jihar Katsina ta koka kan yadda 'yan ta'adda su kayi kaka-gida a wasu kananan hukumomi 8 a jihar

- Kananan hukumomin dai sune Jibia, Batsari, Safana, Dan-Musa, Faskari, Sabuwa, Dandume, Kankara da wasu sassan Kafur

- Gwamnatin jihar ta kafa wani kwamiti na musamman karkashin sakataren gwamnatin jihar domin lalubo hanyoyin magance matsalar

A ranar Laraba da ta gabata ne Gwamna Aminu Bello Masari na jihar Katsina ya sanar da cewa 'yan ta'adda sun mamaye sassa da dama na jihar a wurin taron gaggawa na masu ruwa tsaki a fanin tsaro inda ya ce mutanen jihar sunan cikin hadari har ma da shi.

A yayin da ya ke yiwa manema labarai bayanin wasu abubuwan da aka tattauwa wurin taron, sakataren gwamnatin jihar, Fr. Mustapha Mohammed Inuwa ya gargadin cewa akwai yiwuwar ba za ayi zabe a kananan hukumomi 8 ba muddin ba a dauki mataki ba kamar yadda The Sun ta ruwaito.

'Yan ta'addan sun kwace iko da kananan hukumomi 8 a jihar Katsina

'Yan ta'addan sun kwace iko da kananan hukumomi 8 a jihar Katsina
Source: Depositphotos

DUBA WANNAN: An nadi faifan bidiyon wani malamin islamiyya yana lalata dalibarsa mai shekaru 5

Kananan hukumomin da ya ce 'yan ta'adda da barayin shanu sun mamaye a jihar sun hada da Jibia, Batsari, Safana, Dan-Musa, Faskari, Sabuwa, Dandume, Kankara da wasu sassan Kafur wadda itace karamar hukumar da gwamna ya fito daga.

"Jibia tana da iyaka da Jamhuriyar Nijar inda masu fasakwabri suka artabu da jami'an tsaron Najeriya da Nijar. Wanu abu da yasa samar da tsaro a kananan hukumomin ke da wahala shine yadda suke da iyaka da dajin Rugu wadda yana da fadin kilomita sakwaya 2010. Dajin ya fara ne daga Nijar ya ratsa cikin Katsina har zuwa sassan Jihar Kaduna."

A cewar Mustapha, "Idan ba dauki matakin magance matsalar rashin tsaron ba, zai yi wahala a samu ikon gudanar da zabe a kananan hukumomin 8. Idan ka ce jami'an INEC su tafi zuyi zabe a garuruwan, zaiyi wahala su tafi. Dole mu samar da tsaro kafin zabe."

Wadanda suka hallarci taron sun hada da masu rike da sarautun gargajiya, shugabanin hukumomin tsaro, shugbanin riko na kananan hukumomin da abin ya shafa, masu unguwani da shugabanin addinai.

Mustapha ya ce an yanke shawarar kafa kwamiti da zai jagoranta domin lalubo yadda za a magance matsalar.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel