PDP: Anya kuwa biliyoyin da kake kashewa a jiharka tsaro ake kashewa ko babbar riga?

PDP: Anya kuwa biliyoyin da kake kashewa a jiharka tsaro ake kashewa ko babbar riga?

- Shugaban jam'iyyar PDP na jihar Katsina ya zargi Masari da watanda da dukiyar jiha da sunan tsaro

- Ya kuma kushe cewa da ake APC ta gaji matsalar tsaro dag PDP ne

- Mataimakin gwamnan na musamman ta yada labarai ya kwatanta zargin da siyasa kawai

PDP: Anya kuwa biliyoyin da kake kashewa a jiharka tsaro ake kashewa ko babbar riga?

PDP: Anya kuwa biliyoyin da kake kashewa a jiharka tsaro ake kashewa ko babbar riga?
Source: Facebook

Shugaban jam'iyyar PDP na jihar Katsina, Hon. Salisu Yusuf Majigiri, a jiya ya zargi jam'iyya mai mulki da kuma gwamnatin jihar da laifin kashe biliyoyin Nairori ba tare da kare rayuka da dukiyoyin jama'a ba.

Amma a maida martanin gaggawa da mataimaki na musamman ga gwamna Masari na yada labarai yayi, Abdu Labaran Malumfashi, ya kwatanta zargin da labari mara makama balle tushe.

Majigiri, wanda ya maida martanin maganar da Gwamna Aminu Bello Masari yayi na cewa "Katsina tana zagaye da jami'an tsaro" ya zargi cewa gwamnatin na jefa jihar cikin bashi da matsatsi ta hanyar yin aiyukan da basu gani ba na tsaron jihar Katsina.

PDP: Anya kuwa biliyoyin da kake kashewa a jiharka tsaro ake kashewa ko babbar riga?

PDP: Anya kuwa biliyoyin da kake kashewa a jiharka tsaro ake kashewa ko babbar riga?
Source: Twitter

Shugaban PDP ya shawarci gwamnan da ya gaggauta sauka daga kujerar shi don ba wa mutanen da zasu iya guri don tafiyar da al'amuran jihar.

Yace: "Ina tunanin saukar shi dagq kujerar shi zai kawo maslaha ga jihar Katsina don dama yayi wata 42 ko 43 a cikin watanni 48 da zai yi a mulki. Ana ta kashe biliyoyin kudi akan tsaro amma ba sakamako. Zai fi kyau ya sauka ya ba mutanen dazasu iya tsare rayuka da dukiyoyi guri suyi mulki."

Majigiri ya karyata ikirarin APC na cewa ta gaji rashin tsaro ne daga PDP.

DUBA WANNAN: A 2019, Yawan 'yan gudun hijira a fadin Najeriya yanzu haka ya kai mutum miliyan bakwai

"Ba su gaji rashin tsaro daga PDP ba, koma dai idan sun gada, shugaban kasa Muhammadu Buhari a Akwa Ibom yace ya cika alkawarin shi na samar da tsaro, farfado da tattalin arziki da yaki da rashawa."

Mataimaki na musamman ga gwamnan ya maida martani inda yace "wannan siyasa ce kawai. Lokacin da Majigiri yake shugaban ma'aikatan gwamna Ibrahim Shema, wacce shawara ya bada da fulani suka kashe mutane 142 a Faskari, Sabuwa da Musawa?

Shafin NAIJ.com Hausa ne ya koma LEGIT.ng Hausa

Latsa kuga sabuwar manhajar Legit.ng Hausa a wayarku ta salula: https://play.google.com/store/apps/details?id=ng.legit.hausa&hl=en

Shafukanmu na dandalin sada zumunta sune:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel