Ya kurmantar dani, sannan ya binne danmu ba da sani na ba, mace ta fada wa kotu

Ya kurmantar dani, sannan ya binne danmu ba da sani na ba, mace ta fada wa kotu

- Wata mata ta nemi kotu data raba auran ta da mijinta biyo bayan fada da duka da take samu daga gareshi

- Sanadiyyar dukan da yake mata ya janyo mata matsala a kunnen ta daya wanda ya janyo mata rashin ji

- Bunmi tace mahaifiyar tace take daukar nauyin ciyar da ita tare da ya'yanta

Ya kurmantar dani, sannan ya binne danmu ba da sani na ba, mace ta fada wa kotu

Ya kurmantar dani, sannan ya binne danmu ba da sani na ba, mace ta fada wa kotu
Source: UGC

Wata mata mai suna Mrs Bunmi Segbenu ta nemi kotun dake Badagry dake jihar Legas data kawo karshen auranta da Fetus wanda sukayi aure shekaru 8 da suka gabata.

Matar mai ya'ya Biyu suna zaune a Age-Mowo Badagry ta nemi a raba auran nasu saboda duka da kuma hatsarin da rayuwar ta ke ciki.

Bunmi tace sunyi aure da Festus a shekara ta 2010 ta hanyar biyan cikakken sadaki.

"Festus ya fara fada da dukana bayan na aureshi ba dadewa"

DUBA WANNAN: A 2019, Yawan 'yan gudun hijira a fadin Najeriya yanzu haka ya kai mutum miliyan bakwai

"A yanzu haka banaji da kunne na guda daya saboda dukana da yayi,sannan ya karyamin hannu ya lalatamin waya ta" Bunmi ta bayyanawa kotu.

Ta kara da cewa mahaifiyar ta itace ta dauki nauyin ciyar da ita tare da ya'yanta.

Tace dansu ya kamu da rashin lafiya wanda yayi sanadiyyar mutuwar sa Festus ya binne dan batare daya bari taga gawar yaron ba.

Alkalin kotun Mr Shakirudden Adekola ya dage saurarar wannan kara.

Shafin NAIJ.com Hausa ne ya koma LEGIT.ng Hausa

Latsa kuga sabuwar manhajar Legit.ng Hausa a wayarku ta salula: https://play.google.com/store/apps/details?id=ng.legit.hausa&hl=en

Shafukanmu na dandalin sada zumunta sune:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng News

Mailfire view pixel