Kotu ta zartar da hukuncin rataya kan wasu 'yan fashi da makami 2 a jihar Ondo

Kotu ta zartar da hukuncin rataya kan wasu 'yan fashi da makami 2 a jihar Ondo

A yayin da Hausawa kan ce dan kuka shi ke janyowa Uwar sa jifa, a yau wannan lamari ya kare a kansa domin kuwa mun samu rahoton cewa, ta'adar fashi da makami ta damawa wasu Matasa biyu salalon tsiye kuma dole su kwankwade abinsu a jihar Ondo.

Za ku ji cewa, wata babbar kotun jihar Ondo da ke zamanta a garin Olokuta na babban birnin Akure, ta zartar da mafi girman hukunci kan wasu Matasa biyu da suka aikata mummunan ta'addanci na fashi da makami.

Kotun ba ya tabbatar da laifin miyagun biyu, Tobechukwu Aguonu da kuma Uche Igwe, ta zartar ma su da hukuncin kisa ta hanyar rataya sakamakon munin laifin da suka aikata na fashi da makami.

Kotu ta zartar da hukuncin rataya kan wasu 'yan fashi da makami 2 a jihar Ondo

Kotu ta zartar da hukuncin rataya kan wasu 'yan fashi da makami 2 a jihar Ondo
Source: UGC

Matasan biyu sun gurfana gaban babbar kotun bayan da jami'an tsaro na 'yan sandan jihar Ondo suka cikwikwiye su sakamakon sa hannun su cikin aikata fashi da makami tun a watan Nuwamba na shekarar 2016 da ta gabata.

Laifin Matasan biyu bai wuci fashi da makami da suka yiwa wani mutum, Augustine Okolie, inda suka raba shi da Motar sa, kudade da kuma kadarori daura da kamfanin Katifa ta Olu Foam da ke birnin Akure.

KARANTA KUMA: Rashin tsaro babbar barazana ce ga zaben 2019 - Bincike

Yayin da bincike ya tabbatar da wannan zargi, alkalin Kotun cikin ikon da kuma buwayarsa ta shari'a bisa tanadi na dokokin kasa, mai shari'a Yemi Fasanmi, ya zartar ma su da hukuncin kisa ta hanyar rataya.

Cikin wani rahoton kuma, jaridar Legit.ng ta ruwaito cewa, a madadin koyar da ita harshen larabci, an cafke wani malamin addini dumu-dumu yana tsaka da lalata da wata karamar yarinya 'yar shekara 5 ta dubura a jihar Legas.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da Shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo cikin shafukan mu na zaurukan sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Source: Legit

Mailfire view pixel