Rashin tsaro babbar barazana ce ga zaben 2019 - Bincike

Rashin tsaro babbar barazana ce ga zaben 2019 - Bincike

Baya ga tsantsar adawa ta siyasa da ta mamaye al'ummar kasar nan musamman ta fuskar yada jita-jita da kalaman batanci gami da nuna kiyayya da kuma kalubalantar juna da ta hautsine a tsakanin 'yan takarar kujerar shugaban kasa, rashin tsaro na kuma ci gaba da bujurowa kari bayan kari da ko shakka ba bu zai zamto barazana ga babban zaben kasa da za a gudanar a watan gobe.

A halin yanzu dai wasu sassan kasar nan musamman yankunan Arewa maso Gabas da kuma Arewa maso Yamma, na ci gaba da fuskantar barazana ta rashin tsaro musamman jihar Borno inda tayar da kayar baya na kungiyar Boko Haram ta zamto ciwon ido.

Ko shakka ba bu jihar Borno a kwana-kwanan nan ta fuskanci matsaloli na rashin tsaro a sakamakon mummunar ta'ada da kungiyar Boko Haram ke ci gaba da zartarwa ta hanyar kwanton bauna da kuma shammatar jami'an tsaro.

Lamari na rashin tsaro ya gudana kan harsunan al'umma anan gida da kuma wajen Najeriya dangane da ta'addancin 'yan baranda, barayin shanu, masu fashi da makami da kuma 'yan sara suka da suka addabi jihar Zamfara musamman a shekarar da ta gabata.

Rashin tsaro babbar barazana ce ga zaben 2019 - Bincike

Rashin tsaro babbar barazana ce ga zaben 2019 - Bincike
Source: Depositphotos

A wannan makon kuwa, jihar Katsina da ta kasance Mahaifa ga shugaban kasa Muhammadu Buhari, ta shiga cikin sahun jihohin Najeriya da rashin tsaro ke addabar al'ummar ta, inda gwamnan jihar Aminu Bello Masari, ya yi koken annobar da ta tunkaro al'ummar sa da kuma barazanar ta ga zaben 2019.

Gwamna Masari ya kalubalanci rashin tsaro da cewa ba bu wanda ya tsarkaka da samun kariya a jihar sa sakamakon yadda masu tayar zaune tsaye ke cin karen su ba bu babbaka ko da kuwa a gaban fadar gwamnatin sa.

Yayin tabbatar da wannan lamari, sakataren gwamnatin jihar, Mustapha Inuwa, a jiya Juma'a ya yi furuci na fargabar yadda rashin tsaro zai kasance babbar barazana da za ta tunkari zaben kasa musamman cikin wasu kananan hukumomi takwas da ke fadin jihar.

Kamar yadda majiyar jaridar Legit.ng ta ruwaito, kananan hukumomin da sakataren gwamnatin ya wassafa ma su fama da kalubalai na rashin tsaro sun hadar da Jibia, Batsari, Safana, Danmusa, Kankara, Faskari, Sabuwa da kuma Dandume.

KARANTA KUMA: Ina yiwa Buhari hasashen nasara yayin babban zabe - Guru

Binciken da manema labarai na jaridar Vanguard suka gudanar ya kuma ruwaito cewa, akwai yiwuwar tsagerun Neja Delta za su sake daura damarar su ta tsageranci sakamakon furucin yanke yarjejeniyar su ta ajiye makamai muddin gwamnatin tarayya ta gaza biyan bukatun su.

Duba da yadda rashin tsaro ya yi kamari a jihar Zamfara, gwamnan jihar Abdulaziz Abubakar Yari, ya yi kira kan shimfida dokar ta-baci a jihar da cewa, a shirye yake ya ajiye kambun sa na jagoranci muddin hakan zai tabbatar da tsare lafiya da dukiyar al'ummar sa.

A yayin tuntubar hukumar zabe ta kasa watau INEC, Mista Festus Okoye, jami'inta kan hulda da al'umma ya ce gudanar da zabe a jihar Borno na da tasirin gaske tare raja'a akan hukuncin da hukumar sojin kasa ta zartar akan yiwuwa ko kuma sabanin hakan.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da Shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo cikin shafukan mu na zaurukan sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel