Ina yiwa Buhari hasashen nasara yayin babban zabe - Guru

Ina yiwa Buhari hasashen nasara yayin babban zabe - Guru

Wani fitaccen Malamin duba da ya shahara wajen amfani da Rohanai, Satguru Maharaj Ji, ya yi hasashen nasara ga shugaban kasa Muhammadu Buhari na jam'iyya mai ci ta APC a yayin babban zaben kasa da za a gudanar a watan gobe.

Guru da ya ce yana kyautata zaton shugaba Buhari zai lallasa sauran 'yan takarar kujerar shugaban kasa yayin babban zabe da suka hadar har da dan takara na babbar jam'iyyar adawa ta PDP, Atiku Abubakar.

Ko shakka ba bu shugaban kasa Buhari, Atiku, wani tsohon Ministan Ilimi, Oby Ezekwesili, Mista Omoyele Sowore da kuma wasu 'yan takara 72 za su fafata a zaben shugaban kasa da za a gudanar a ranar 16 ga watan Fabrairu na gobe.

Ina yiwa Buhari hasashen nasara yayin babban zabe - Guru

Ina yiwa Buhari hasashen nasara yayin babban zabe - Guru
Source: UGC

Sai dai Guru cikin jawaban da ya gabatar yana tsaka da ganawa da manema labarai yayin bikin cikarsa shekaru 39 da hallara a Najeriya, ya yi ikirarin cewa ya leka ya hango shugaba Buhari zai yi nasara da kuri'u masu tarin yawa fiye da na sauran 'yan takara.

Yayin amintuwa da hasashen sa, Guru ya ce bai hangi wata nasara ga sauran 'yan takara ba irin su Atiku, Ezekwesili, Sowore da sauransu. Ya ce al'ummar Najeriya su fito kwansu da kwarkwata wajen kadawa Buhari kuri'un su domin kuwa yayi kwazo da bajinta sama da ta magabatan sa.

KARANTA KUMA: Hukumar Kwastam ta tara kudin haraji na N1.2tn, ta yi wawan kamu 5,235 a shekarar 2018

Cikin wani rahoton mai nasaba da wannan, kungiyar Kiristoci reshen Arewacin Najeriya, ta ce ba bu ita ba bu goyon bayan kudirin tazarce na Buhari a babban zaben kasa da za a gudanar a watan gobe.

Kazalika jaridar Legit.ng ta ruwaito cewa, dan takarar kujerar shugaban kasa na jam'iyyar PDP, Atiku, ya nemi gwamnan jihar Zamfara, Abdulaziz Abubakar Yari da ya yi murabus kan rashin tsaro da ya yiwa jihar sa katutu.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da Shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo cikin shafukan mu na zaurukan sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Source: Legit

Mailfire view pixel