Karshen duniya: An hasko bidiyon wani malami na lalata da 'yar shekaru 5 ta dubura

Karshen duniya: An hasko bidiyon wani malami na lalata da 'yar shekaru 5 ta dubura

- Rundunar 'yan sanda ta samu nasarar cafke wani malami, mai shekaru 43, bisa zarinsa da yin lalata da wata yarinyar mai shekaru 5 ta dubura a cikin wani masallaci

- Rundunar 'yan sanda ta tabbatar da cewa, ba wannan bane karo na farko da aka kama malamain yana aikata irin wannan aika-aikar

- Wanda ake zargin, Abdusalam Salaudeen, ya amince da aikata wannan laifi da ake zarginsa da shi, inda rundunar ta ce zata gurfanar da shi gaban kotu

Rundunar 'yan sanda ta samu nasarar cafke wani malami, mai shekaru 43, bisa zarinsa da yin lalata da wata yarinyar mai shekaru 5 ta dubura a cikin wani masallaci, a unguwar Igando, jihar Legas. Rundunar 'yan sanda ta ce an ga bidiyon Abdusalam Salaudeen yana fasa duburar yarinyar, wacce ya kamata ace yana koyar da ita yaren Larabci.

Rundunar 'yan sanda ta tabbatar da cewa, ba wannan bane karo na farko da aka kama malamain yana aikata irin wannan aika-aikar, wanda har makwabta suka samu nasarar daukarsa bidiyo a lokacin da yake haikewa yarinyar.

Mai magana da yawun rundunar 'yan sanda ta jihar Legas, Chike Oti, wanda ya tabbatar a faruwar lamarin, ya ce a ranar 28 ga watan Disamba, wani mai kishin kasa, ya garzaya ofishin hukumar dauke da bidiyo, wanda ya tabbatar da Alfa, na lalata da yarinyar mai shekaru 5 ta dubura.

KARANTA WANNAN: Dino Melaye na asibitin hukumarmu, cikin koshin lafiya - Rundunar 'yan sanda

Karshen duniya: An hasko bidiyon wani malami na lalata da 'yar shekaru 5 ta dubura

Karshen duniya: An hasko bidiyon wani malami na lalata da 'yar shekaru 5 ta dubura
Source: Twitter

Oti ya ce wanda ya kawo karar, ya bukaci ganawa da kwamishinan 'yan sanda na jihar, CP Edgal Imohimi. Inda hankalin kwamishinan ya tashi bayan kallon bidiyon, tare da bada umurnin cafko wanda ake zargin da mikashi ga sashen bincike na musamman don daukar mataki.

Ya ce jami'n hukumar basu bata lokaci ba, suka bazama nemansa, inda suka samu nasarar cafke shi a kusa da wani masallaci da ke unguwar Igando, da ke jihar.

"Ko da yaga ya shiga hannu, kamar wani mai wasan kwaikwayi, ya zube kasa, yana kuka tare da neman gafara, yana mai amsa laifinsa. Daga baya ya fadi sunansa Abdulsalam Salaudeen, mai shekaru 43 wanda ke da zama a gida mai lamba 16, titin Awoyemi, unguwar Igando, Ikotun, Legas.

"Da zaran hukumar ta kammala bincike, za a gurfanar da wanda ake zargin gaban kotu," a cewar Oti.

SANARWA: Shafin jaridar NAIJ.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa. Muna fatan za ka ci gaba da kasancewa tare da Legit.ng Hausa don karanta labarai da dumi duminsu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel