Hukumar Kwastam ta tara kudin haraji na N1.2tn, ta yi wawan kamu 5,235 a shekarar 2018

Hukumar Kwastam ta tara kudin haraji na N1.2tn, ta yi wawan kamu 5,235 a shekarar 2018

Za ku ji cewa, hukumar yaki da kuma hana fasakauri ta Najeriya da aka fi sani da hukumar Kwastam, a jiya Juma'a, ta yi karin haske dangane da adadin dukiya ta kudin haraji da ta tarawa gwamnatin tarayyar Najeriya cikin shekarar bara.

Majiyar rahoton ta shafin jaridar The Punch ta bayyana cewa, hukumar yaki da fasaukari ta Najeriya ta tarawa gwamnatin tarayyar Najeriya zunzurutun dukiya ta kudin haraji na Naira Tiriliyan 1.2 cikin shekarar 2018 da ta gabace mu.

Babban kakakin hukumar na kasa, Mista Joseph Attah, shine ya bayar da shaidar hakan cikin wata sanarwa yayin ganawar sa da manema labarai a ranar da ta gabata cikin babban birnin kasar nan na tarayya.

Wannan adadi na Naira tiriliyan 1.2 ya samu doriyar Naira biliyan 164.89 bisa kudin haraji na Naira tiriliyan 1.03 da hukumar kwastam ta tarawa gwamnatin tarayyar kasar nan a shekarar 2017 da ta gabata.

Kwanturola Janar na hukumar Kwastam, Kanal Hameed Ali mai ritaya

Kwanturola Janar na hukumar Kwastam, Kanal Hameed Ali mai ritaya
Source: Depositphotos

Kwanturola Janar na hukumar, Kanal Hameed Ali mai ritaya, ya yabawa wannan kwazo tare jinjina kan wannan bajinta da hukumar ta yi a sakamakon shimfidar kyawawan tsare-tsare domin inganta harkokin su na gudanarwa ta kowace fuska.

Kanal Ali ya ke cewa, wannan tsare-tsare sun yi tasirin gaske tare da bayar da gudunmuwa wajen taka muhimmiyar rawar gani domin ci gaban kasa da ya zamana daya daga cikin akidun gwamnatin shugaban kasa Muhammadu Buhari.

Cikin sanarwar da hukumar ta bayar, ta kuma samu nasarar dakile wasu ababe na faskauri inda tayi wawan kamu kimanin 5,235 da kudin harajin su ya tasar ma Naira biliyan 61.54 kamar yadda majiyar jaridar Legit.ng ta ruwaito.

KARANTA KUMA: Matasa: Ku fara shirin rike akalar jagoranci - Buhari

Ire-iren ababe na fasakauri da hukumar ta samu nasarar datsewa na haramtattun kayayyaki sun hadar da muggan makamai, miyagun kwayoyi mara su Tramadol da kuma buhun shinkafa 320,709 da aka ratsao da su daga kasashen ketare.

Hukumar ta kuma yi kira na neman goyon baya ga dukkanin ma su ruwa da tsaki akan hada hannu tare gwiwa wajen inganta harkokinta gami da cimma manufofi da kudirin ta a wannan shekara ta 2019.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da Shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo cikin shafukan mu na zaurukan sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Source: Legit Newspaper

Mailfire view pixel