Dino Melaye na asibitin hukumarmu, cikin koshin lafiya - Rundunar 'yan sanda

Dino Melaye na asibitin hukumarmu, cikin koshin lafiya - Rundunar 'yan sanda

- Rundunar 'yan sanda ta ce Sanata Dino Melaye, wanda ya fadi sumamme a ranar Juma'a a ofishinsu, awanni kadan bayan da ya mika kansa ga hukumar

- Sai dai rundunar 'yan sanda ta ce lafiyar Dino Melaye kalau, bayan kaishi asibitin

- Rundunar ta ce da zaran an kammala bincike, za a gurfanar da shi gaban kotu, don yanke masa hukunci kan aikata laifin yunkurin kisan kai

Rundunar 'yan sanda ta ce Sanata Dino Melaye, wanda ya fadi sumamme a ranar Juma'a a ofishinsu, sakamakon zargin azabtar da shi da jami'anta suka yi, awanni kadan bayan da ya mika kansa ga hukumar, a halin yanzu na asibitin rundunar da ke Abuja.

Sai dai rundunar 'yan sanda ta ce lafiyar Dino Melaye kalau, bayan kaishi asibitin.

Jami'in hulda da jama'a na rundunar, Jomoh Moshood, a cikin wata sanarwa a safiyar Asabar, uya ce Sanatan, wanda a baya aka bayyana shi a matsayin wanda hukumar ke nema ruwa a jallo bisa zargin yunkurin aikata kisan kai, zai gurfana gaban kotu da zan rundunar ta kammala bincike akan zargin da ake masa.

KARANTA WANNAN: Da ace Buhari zai waiwayi fannin lantarki, da Obasanjo ya koma magarkama - Oshiomhole

Dino Melaye na asibitin hukumarmu, cikin koshin lafiya - Rundunar 'yan sanda

Dino Melaye na asibitin hukumarmu, cikin koshin lafiya - Rundunar 'yan sanda
Source: Facebook

Sanarwar ta bayyana cewa Sanata Dino Melaye wanda "aka bayyana shi a matsayin wanda ake nema ruwa a jallo sakamakon yunkurin kisan kai a ranar 19 ga watan Yulin 2018, a lokacin da shi da 'yan bangar siyasarsa, suka kaiwa wani Sajen Danjuma Saliu hari, tare da harbinsa a bakin aiki, kan hanyar Aiyetoro zuwa Gbede, a jihar Kogi."

Sanarwar ta ce Sanatan ya mika wuyansa bayan shafe kwanaki 8, jami'an rundunar na girke a gaban gidansa. Tun a ranar 28 ga watan Disamba 2018, da misalin karfe 10 na safiya, jami'an rundunar 'yan sanda suka dira a gidan Melaye, dauke da takardar bada izinin kamu akan zargin yunkurin kisan kai.

"A halin yanzu dai Sanata Dino Melaye na asibitin hukumarmu, inda kuma tuni aka fara gudanar da bincike kan wannan zargi da ake masa. Yana cikin koshin lafiya. Da zaran an kammala bincike, za a gurfanar da shi gaban kotu, don yanke masa hukunci kan aikata laifin yunkurin kisan kai," cewar sanarwar.

SANARWA: Shafin jaridar NAIJ.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa. Muna fatan za ka ci gaba da kasancewa tare da Legit.ng Hausa don karanta labarai da dumi duminsu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel