Da ace Buhari zai waiwayi fannin lantarki, da Obasanjo ya koma magarkama - Oshiomhole

Da ace Buhari zai waiwayi fannin lantarki, da Obasanjo ya koma magarkama - Oshiomhole

- Mr Adams Oshiomhole, ya ce Olusegun Obasanjo ba zai tsalake hukunci ba, ma damar Buhari ya kudiri aniyar binciken fannin wutar lantarki

- Oshiomhole ya ce Obasanjo da Atiku sun batar da $16bn akan wutar lantarki, bayan shekaru 8, sai duhu ya kara mamaye Nigeria mai makon hasken lantarki a Nigeria

- Oshiomhole ya bayyana takaicinsa akan yadda wadanda suka lalata fannin wutar lantarki, yanzu kuma sun dawo da burin son sake shugabantar kasar

Shugaban jam'iyyar APC na kasa, Mr Adams Oshiomhole, a ranar Juma'a ya ce tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo ba zai tsalake hukunci ba, ma damar shugaban kasa Muhammadu Buhari ya kudiri aniyar binciken fannin wutar lantarki.

Tsohon gwamnan jihar Edo, ya bayyana hakan ne a garin Jos, a wajen taron kaddamar da yakin zaben gamnan jihar Filato, Simon Lalong a karo na biyu, wanda ya gudana a babban filin wasanni na Rwang Pam.

Ya ce: "A 1999, Obasanjo ya ce idan har aka zabe shi a matsayin shugaban kasa, sai Atiku Abubakar a matsayin mataimaki, zai gyara fannin lantarki cikin watanni 6, kuma za a samu hasken lantarki a fadin Nigeria. Sai bayan shekaru ne muka fahimci inda ya dosa.

KARANTA WANNAN: Kaji gaskiya: Babu dan fansho da ke bin gwamnatina bashi, an biya kowa hakkinsa - Buhari

Da ace Buhari zai waiwayi fannin lantarki, da Obasanjo ya koma magarkama - Oshiomhole

Da ace Buhari zai waiwayi fannin lantarki, da Obasanjo ya koma magarkama - Oshiomhole
Source: Depositphotos

"Shi da mataimakinsa sun batar da $16bn akan wutar lantarki, bayan shekaru 8, sai duhu ya kara mamaye Nigeria mai makon alkawarin hasken lantarkin da suka yiwa 'ya Nigeria a lokacin yakin zabensu. Don haka idan shugaban kasa Buhari ya ce zai waiwayi fannin lantarki, tabbas Obasanjo zai koma magarkama, saboda irin badakalar da yayi da kudin kasar."

Oshiomhole ya bayyana takaicinsa akan yadda wadanda suka lalata fannin wutar lantarki da sauran fannonin tattalin arzikin kasar, sune kuma suka dawo yanzu da burin son sake shugabantar kasar.

Ya bukaci 'yan Nigeria da su kauracewa zaben irin wadannan mutanen a zabe mai zuwa, don baiwa kasar damar cimma kudurinta na gogayya da sauran kasashen duniya.

Ya ce: "Shi Atiku asalinsa jami'in kwastam ne, shi kuma Peter Obi dan kasuwa ne. Wannan tikitin takarar nasu, wani shiri ne na Obasanjo da jam'iyyarsa ta PDP. Ba zasu taba canja zani ba. Tuni har Atiku ya ce zai sayar da kamfanin NNPC idan aka zabe shi. Na tabbata idan aka zabe shi, zai sayar da kasar ne gaba daya. Don haka ya kamata 'yan Nigeria su yiwa kansu karatun ta-nutsu a zaben 2019."

SANARWA: Shafin jaridar NAIJ.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa. Muna fatan za ka ci gaba da kasancewa tare da Legit.ng Hausa don karanta labarai da dumi duminsu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Source: Legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel