Iyalai dake zargin mata da kashe musu dan'uwa sun kufulo, suna neman fansa

Iyalai dake zargin mata da kashe musu dan'uwa sun kufulo, suna neman fansa

- Ana tuhumar wata mata da kashe mijinta

- Iyalan wanda aka kashe din sunce matar ta bugawa dan uwansu abu a kai bayan wata jayyaya da sukayi a tsakanin su

- Kafin mutuwar tashi sunje ofishin yan sanda mafi kusa dasu akan rigimar tasu

Iyalai dake zargin mata da kashe musu dan'uwa sun kufulo, suna neman fansa

Iyalai dake zargin mata da kashe musu dan'uwa sun kufulo, suna neman fansa
Source: Depositphotos

Hukumar yan sanda ta kama wata mata mai suna Folashade Komolafe bisa zargin cewa ta kashe mijinta mai suna John Oloye.

Iyalan wanda aka kashe din sunce Komolafe ta bugawa dan ruwan nasu abu a kai bisa ga wata jayayya da sukayi a tsakanin su a ranar 30 ga watan Disemba 2018 a gidan su dake Bunmi Ajakaye street dake jihar Legas.

Dan uwan wanda aka kashe din Felix wanda yayi magana a madadin ragowar yan uwa yace Oloye ya kirashi da misalin 11:30pm yake sanar dashi cewa shi da matarshi suna ofishin yan sanda saboda matsalar.

Felix yace sunyi magana da wani jami'in dan sanda inda yace masa an sasantasu sun tafi gida.

Amma daga baya wani abokin Oloye ya kara kiran shi da misalin 4am inda yake shaida masa mutuwar dan uwan nashi dan shekara 38.

DUBA WANNAN: A 2019, Yawan 'yan gudun hijira a fadin Najeriya yanzu haka ya kai mutum miliyan bakwai

Masu kawo mana rahoto sun bayyana cewa anyi gaggawar mika Oloye zuwa wani asibitin kudi sukaki karbar sa inda ya mutu akan hanyar su ta kaishi babban asibiti na Idimu.

Felix yace abinda ya bashi mamaki shine har zuwa yanzu hukumar yan sandan bata mika wannan mata hannun hukumar SCIID ba wanda baisan dalilin wannan jinkiri ba.

A halin yanzu an mika gawar Oloye zuwa babban asibitin Badagry don binciken musabbabin mutuwar tashi.

Shafin NAIJ.com Hausa ne ya koma LEGIT.ng Hausa

Latsa kuga sabuwar manhajar Legit.ng Hausa a wayarku ta salula: https://play.google.com/store/apps/details?id=ng.legit.hausa&hl=en

Shafukanmu na dandalin sada zumunta sune:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel