Jami'an kwastam sun cafke motar Dangote makare da haramtattun kayayyaki a Arewa

Jami'an kwastam sun cafke motar Dangote makare da haramtattun kayayyaki a Arewa

Jami'an hukumar hana fasa kwauri ta kasar Najeriya sun sanar da samun nasarar cafke wata motar Dangote da ke dakon siminti makare da haramtacciyar shinkafa a jihar Adamawa dake a shiyyar Arewa maso gabashin Najeriya.

Kwanturolan jami'an kwastam din shiyyar jihar ta Adamawa da Taraba Kamardeen Olumoh ne ya bayyana hakan lokacin da yake zagayawa da 'yan jarida a harabar rundunar domin nuna masu irin kamen da suka yi a cikin kankanin lokaci.

Jami'an kwastam sun cafke motar Dangote makare da haramtattun kayayyaki a Arewa

Jami'an kwastam sun cafke motar Dangote makare da haramtattun kayayyaki a Arewa
Source: UGC

KU KARANTA: Yan sanda sun fadin abun da za suyi wa Dino Melaye

Legit.ng Hausa ta samu cewa Kwanturolan ya kara da cewa jami'an sa sun cafke motar ta Dangote ne dauke da buhunna 150 na haramtacciyar shinkafar da aka hana shigowa da ita cikin kasar bayan da direban motar ya tsere.

Mista Olumoh ya kara da cewa shinkafar da aka kama ta na da kudaden harajin da ya kai adadin Naira miliyan 59.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma legit.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://web.facebook.com/legitnghausa?_rdc=1&_rdr

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel