'Yan sanda sun fadi abunda za suyiwa Dino Melaye da an sallame shi daga asibiti

'Yan sanda sun fadi abunda za suyiwa Dino Melaye da an sallame shi daga asibiti

Jami'an 'yan sandan Najeriya sun bayyana cewa da zarar an sallami Sanata Dino Melaye daga asibiti za su kai shi kotu gaban alkali idan sun kammala bincike domin cigaba da tuhumar sa da suke yi.

Wannan dai na kunshe ne a cikin wata sanarwar manema labarai da Jami'in hulda da jama'a na hukumar 'yan sanda, Jimoh Moshood ya fitar da yammacin yau.

'Yan sanda sun fadi abunda za suyiwa Dino Melaye da an sallame shi daga asibiti

'Yan sanda sun fadi abunda za suyiwa Dino Melaye da an sallame shi daga asibiti
Source: Facebook

KU KARANTA: Yan bindiga sun sake kai hari Zamfara

Legit.ng Hausa ta samu cewa majiyar mu ta Channels TV ta ce an garzaya da Sanata Dino Melaye zuwa asibitin 'yan sanda da ke Garki Area 1 a Abuja bayan an damke shi an kai shi hedkwatan 'yan sanda na SARS.

Daya daga cikin jami'an 'yan sandan da ke cikin tawagar da suka dabaibaye gidan Dino Melaye a Abuja ne ya tabbatar sanar da hakan.

Dan sandan ya ce a halin yanzu an bawa Sanata Melaye gado a asibiti domin ya huta kafin hukumar 'yan sandan ta dauki mataki na gaba.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma legit.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://web.facebook.com/legitnghausa?_rdc=1&_rdr

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Source: Legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel