Kaji gaskiya: Babu dan fansho da ke bin gwamnatina bashi, an biya kowa hakkinsa - Buhari

Kaji gaskiya: Babu dan fansho da ke bin gwamnatina bashi, an biya kowa hakkinsa - Buhari

- Shugaban kasa Muhammadu Buhari, ya bugi kirji da cewa gamnatinsa ta kawo karshen duk wasu matsaloli da 'yan fanshon gwamnatin tarayya ke fuskanta a kasar

- Buhari ya yi nuni da cewa an biya duk wasu basussukan da 'yan fansho ke bi, haka zalika ana biyansu hakkonkinsu akan lokaci

- Ya ce walwalar 'yan fansho na da muhimmanci a gwamnatinsa tun daga watan Mayu, 2015

A ranar Juma'a, shugaban kasa Muhammadu Buhari, ya bugi kirji da cewa gamnatinsa ta kawo karshen duk wasu matsaloli da 'yan fanshon gwamnatin tarayya ke fuskanta a kasar, tare da cewar walwalar 'yan fansho na da muhimmanci a gwamnatinsa tun daga watan Mayu, 2015.

Shugaban kasa Muhammadu Buhari tare da uwar-gidansa Hajiya Aisha Buhari a lokacin da suke zantawa da wata tawaga ta kungiyar 'yan fansho ta kasa NUP, karkashin jagorancin shugaban kungiyar, Kwamred Buhari Musa Ayuba Dallatu, a fadar shugaban kasa, Buhari ya yi nuni da cewa an biya duk wasu basussukan da 'yan fansho ke bi, haka zalika ana biyansu hakkonkinsu akan lokaci.

Ya ce wadanda suka yi ritaya, suna bukatar hakkokinsu akan lokaci, tare da samun girmamawa bisa aikin da suka shafe tsawon shekaru na rayuwarsu suna yi, duk don ci gaban kasar.

KARANTA WANNAN: Da duminsa: An tashi baran-baran a zaman tattaunawar NLC da gwamnatin tarayya

Kaji gaskiya: Babu dan fansho da ke bin gwamnatina bashi, an biya kowa hakkinsa - Buhari

Kaji gaskiya: Babu dan fansho da ke bin gwamnatina bashi, an biya kowa hakkinsa - Buhari
Source: Depositphotos

"A shekarun da suka shude, an mayar da 'yan fanshi saniyar ware, an mayar da su kamar ba wadanda suka shafe shekaru masu yawa suna yiwa gwamnati aiki ba, sam ba a damuwa da matsalolinsu. To a yanzu, mun kawo karshen wannan."

"Kamar yadda ku da kawunanku a yau kuka tabbatar, mun soma biyan hakkokin 'yan fansho kowanne wata akan lokaci, tare da biya sauran basussukan da suke bi.

Gwamnatin tarayya ta saki N45bn don kaddamar da shirin nan na 'yan fansho, haka zalika an saki N22.4bn don biyan tsofaffin ma'aikatan sufurin jiragen sama hakkokinsu da basussukan da suke bi," a cewar Buhari.

Shugaban kasa Buhari, ya shaidawa 'yan fansho cewa gwamnatin tarayya ta sakarwa jihohi kudaden Bail Out, don biyan albashi da basussukan 'yan fansho, daga kudin Paris Club, kuma ya bayar da umurni na kaddamar da shirin farfado da kamfanin karafa na 'yan fansho da ke Niger Delta, NITEL/MTEL da sauran abubuwan da suka shafi 'yan fansho na kasar.

SANARWA: Shafin jaridar NAIJ.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa. Muna fatan za ka ci gaba da kasancewa tare da Legit.ng Hausa don karanta labarai da dumi duminsu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Source: Legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel