Wata sabuwa: An cafke wani malami dake saida tikitin shiga aljanna $500

Wata sabuwa: An cafke wani malami dake saida tikitin shiga aljanna $500

Mun samu labarin cewa jami'an 'yan sandan kasar Zimbabwe sun cafke wani babban Fasto mai suna Tito Watts da matar sa Amanda dake damfarar jama'ar kasar suna saida masu tikitin zuwa aljanna akan kudi $500 dake dai dai da Naira 181,000.

Kamar dai yadda muka samu, an ce kuma tikitin da yake saidawa 'yan majami'ar ta sa yace mutum ba zai fuskanci hisabi ba indai har ya bashi shi.

Wata sabuwa: An cafke wani malami dake saida tikitin shiga aljanna $500

Wata sabuwa: An cafke wani malami dake saida tikitin shiga aljanna $500
Source: UGC

KU KARANTA: Babban dalilin da yasa ba mu son Buhari - Gwamnan Benue

Legit.ng Hausa ta samu cewa tikitin da Fasto Tito Watts yake siyarwa an yi shi ne da mulmulallen zinari kuma yace dukkan wanda ya mallaki tikitin to yana da wuri na musamman a can aljannar ta shi.

Da yake fira da manema labarai, Fasto Tito Watts ya kara da cewa shi baya tsoron dukkan wani jami'in tsaro kuma a ganin sa ba dalilin da za'a kama shi domin bai yi laifin komai ba.

Ya kara da cewa Allah ne yayi masa manuniya game da yayi hakan domin samun kudaden shiga da kuma taimakon 'yan kasar.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma legit.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://web.facebook.com/legitnghausa?_rdc=1&_rdr

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel