Da duminsa: An tashi baran-baran a zaman tattaunawar NLC da gwamnatin tarayya

Da duminsa: An tashi baran-baran a zaman tattaunawar NLC da gwamnatin tarayya

- An tashi baran-baran ba tare da cimma wata matsaya ba a zaman da kungiyar NLC ta yi da gwamnatin tarayya

- An gudanar da zaman ne don sanin matakan da za abi don hana kungiyoyin kwadago shiga yajin aikin da suka kuduri niyyar farawa ranar 8 ga watan Janairu

- Taron dai ya fara ne da misalin karfe 12:50 na rana, inda aka je hutu da misalin karfe 3:20 na rana, kana aka koma karo na biyu da misalin karfe 4:28 na yamma

Zaman tattaunawar da aka shirya don hana kungiyar kwadago ta kasa NLC shiga yajin aikin da ta shirya zuwa ranar 8 ga watan Janairu, ya kare ba tare da an cimma wata matsaya guda daya ba, tsakanin gwamnatin tarayar da kungiyar NLC.

Wannan yajin aiki da kungiyoyin kwadago na kasar suka kudiri farawa, ya ta'allaka ne akan nunawa shugaban kasa Muhammadu Buhari muhimmancin mikawa majalisar dokokin tarayya dokar sabunta albashi mafi karanci zuwa N30,000 ga ma'aikatan kasar.

A yayin da yake ganawa da manema labarai a yammacin ranar Laraba, shugaban kungiyar NLC na kasa, Ayuba Wabba, ya ce an dage zaman ne har sai ranar Litinin, da misalin karfe 5 na yamma.

KARANTA WANNAN: CUPP: Dalilin da yasa Buhari ke son IGP Idris yaci gaba da sugabantar hukumar 'yan sanda

Da duminsa: An tashi baran-baran a zaman tattaunawar NLC da gwamnatin tarayya

Da duminsa: An tashi baran-baran a zaman tattaunawar NLC da gwamnatin tarayya
Source: UGC

A nashi bangaren, ministan kwadago, Chris Ngige, wanda ya jagoranci tawagar gwamnatin tarayya a zaman sulhun, ya ce gwamnati ta fara shawo kan ma'aikatan.

Taron dai ya fara ne da misalin karfe 12:50 na rana, inda aka je hutu da misalin karfe 3:20 na rana, kana aka koma karo na biyu da misalin karfe 4:28 na yamma.

An je hutun rabin lokaci ana tsakiyar yin taron ne saboda kiran gaggawa da shugaban kasa Muhammadu Buhari yayiwa Mr Ngige, ministar kudi, Zainab Ahmed, da kuma ministan kasafin kudi, Udoma Udoma, don yin wata ganawar gaggawa a fadar shugaban kasa.

SANARWA: Shafin jaridar NAIJ.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa. Muna fatan za ka ci gaba da kasancewa tare da Legit.ng Hausa don karanta labarai da dumi duminsu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Source: Legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel