Tashin hankali: Wani mutum ya cinna wa kansa wuta saboda matar sa tayi yaji

Tashin hankali: Wani mutum ya cinna wa kansa wuta saboda matar sa tayi yaji

Wani magidanci mai shekaru 40, Abdullahi Jafaru ya yi yunkurin kashe kansa bayan matarsa, Halima tayi yaji sakamakon sabani da suka samu da shi a cewar 'yan sanda.

A cewar 'yan sandan, Abdullahi ya balbale jikinsa da fetur ne sannan ya cinna ma kansa wuta.

Mai magana da yawun 'yan sandan jihar Jigawa, Audu Jinjiri ya ce a ranar 31 ga watan Disamban 2018 ne Halima tayi yaji daga gidan mijinta saboda wani sabani da ya shiga tsakaninsu.

'Yan sanda sun gano cewa Mr Jafaru mazaunin kauyen Shunar ne da ke karamar hukumar Kafin Hausa na jihar ta Jigawa.

Tashin hankali: Wani mutum ya cinna wa kansa wuta saboda matar sa tayi yaji

Tashin hankali: Wani mutum ya cinna wa kansa wuta saboda matar sa tayi yaji
Source: Twitter

DUBA WANNAN: An dakatar da 'yan majalisun Zamfara guda 4 saboda tuburewa Gwamna Yari

Mr Jinjiri ya ce Mr Ja'afaru ya yi kokarin shawo kan amaryarsa, Halima da dawo gidansa amma hakan bai yiwu ba.

An ruwaito cewa ma'auratan suna da yara shida.

Bayan ya gaza shawo kan matarsa da dawo gida, Mr Abdullahi ya zuba fetur a jikinsa kuma ya cinna ma kansa wuta.

"'Yan sanda sun garzaya unguwar da ya ke cikin gagawa bayan sun sami labarin kuma suka ceto rayuwarsa suka kai shi asbiti.

"Sai dai ko da ya ke jinya a gadon asibiti, Mr Jafaru bai dena kirar sunan amaryarsa Halima ba duk da cewa uwargidansa tana tare dashi a asibitin tana jinyarsa," inji mai magana da yawun 'yan sandan.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel