2019: Za a gwabza ne tsakanin rikakkun Barayi da Talakawa – Amaechi

2019: Za a gwabza ne tsakanin rikakkun Barayi da Talakawa – Amaechi

Darekta Janar na kwamitin yakin neman zaben shugaba Muhammadu Buhari, watau Rotimi Chibuike Amaechi, ya bayyana cewa zaben da za ayi a Kwara da kasa baki daya zai sa mulki ya dawo hannun talakawa.

2019: Za a gwabza ne tsakanin rikakkun Barayi da Talakawa – Amaechi

Rotimi Chibuike Amaechi yace mutanen PDP manyan Barayi ne
Source: Depositphotos

Rotimi Chibuike Amaechi wanda shi ne shugaban yakin neman zaben Buhari da Osinbajo a 2019 ya fadawa mutanen Kwara su sha kurumin su a zabe mai zuwa inda yace Talakawa za su karbe mulkin jihar a karkashin jam’iyyar APC.

Rotimi Amaechi ya bayyana wannan ne a Garin Ilorin, a jihar Kwara lokacin da da su ke yawon yakin neman zabe. Amaechi yace barayin kasar nan sun koma jam’iyyar PDP inda su ke ta faman yakar shugaba Muhammadu Buhari a APC.

KU KARANTA: An gyara makarantun Boko 1, 024 daga 2015 zuwa yanzu – Gwamnan APC

Babban Ministan sufurin kasar wanda yake kokarin ganin APC ta zarce kan mulki, ya fadawa mutanen Kwara cewa burin jam’iyyar APC shi ne ganin mulki ya bar hannun mala’u, ya koma hannun Talakawan kasar nan a zaben bana na 2019.

Sauran jiga-jigan APC irin su ministan yada labarai, Alhaji Lai Mohammed, su na cikin wanda su ka leka jihar ta Kwara. Kusoshin na APC sun bayyanawa mutanen jihar cewa banbancin su da sauran jam’iyya shi ne, APC na kokarin gyara kasa.

Shugaban majalisar dattawa, Bukola Saraki ya fito ne daga jihar Kwara. Yanzu Bukola Saraki ya sauya-sheka daga APC zuwa jam’iyyar PDP a 2018 inda ake sa rai za su fafata a zaben da za ayi a bana.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Source: Legit

Mailfire view pixel