CUPP: Dalilin da yasa Buhari ke son IGP Idris yaci gaba da sugabantar hukumar 'yan sanda

CUPP: Dalilin da yasa Buhari ke son IGP Idris yaci gaba da sugabantar hukumar 'yan sanda

- Kungiyar CUPP ta ce shugaban kasa Buhari na kulla makircin barin IGP Idris ya ci gaba da shugabanta hukumar 'yan sanda don tafka magudi a zaben 2019

- CUPP ta kuma yi zargin cewa fadar shugaban kasa, APC da jami'an tsaro, sun shirya tsaf don tabbatar da tazarcen Buhari ko ta halin kaka

- Kungiyar ta bukaci Buhari da ya mayar da hankali akan rayuwakan 'yan Nigeria da ake kashewa a wasu jihohi na kasar, mai makon dagewa akan nasarar yin tazarce

Gamayar kungiyoyin siyasa, CUPP karkashin inuwar jam'iyyun adawa na kasar, sun zargi shugaban kasa Muhammadu Buhari da kulla makircin da zai sanya Sifeta Janar na rundunar 'yan sanda Ibrahim Idris, ya ci gaba da shugabantar hukumar rundunar 'yan sanda duk da cewa wa'adinsa ya kare, domin samun damar taimaka mashi wajen tafka magudi a zabukan 2019 da ke gabatawo.

Kungiyar CUPP, a cikin wata sanarwa, ta hannun kakakinta, Ikenga Ugochinyere, ta kuma yi zargin cewa akwai wata kullalliya da ake kitsawa tsakanin fadar shugaban kasa, APC da hukumomin tsaro wajen sanar da sakamakon zabe na karya.

A cewar CUPP, idan har gwamnatin ta samu nasarar tafka magudi, kuma jama'ar Nigeria suka nuna bacin ransu tare da yin zanga zanga, to akwai zargin gwamnatin zata yi amfani da jami'an tsaro wajen tursasa mutane amincewa da sakamon.

KARANTA WANNAN: Yanzu yanzu: IGP Idris ya yi biris da Dino Melaye a shelkwatar rundunar 'yan sanda

CUPP: Dalilin da yasa Buhari ke son IGP Idris yaci gaba da sugabantar hukumar 'yan sanda

CUPP: Dalilin da yasa Buhari ke son IGP Idris yaci gaba da sugabantar hukumar 'yan sanda
Source: UGC

Sanarwar ta ja hankalin 'yan Nigeria akan wani bita da kulli da gwamnatin shugaban kasa Buhari take yi na tura jami'an soji a fadi kasar gabanin zabukan 2019 da ke gabatowa.

Haka zalika, kungiyar gamayyar jam'iyyun siyasar sun yi zargin cewa hukumar zabe mai zaman kanta na iya zama karen farauta ga gwamnatin Buhari, inda za a yi amfani da ita wajen sauya sakamakon zabe.

Ta ce: "Mun samu rahoto daga majiya mai tushe, cewar bayan amfani da jami'an tsaro wajen magudin zaben 2019, Hajiya Amina Zakari, ta shigo da wasu kwamishinonin hukumar INEC da jami'ai, wadanda ake ba horo yanzu haka, don taimakawa gwamnati wajen tafka magudi.

"Haka zalika, akwai wasu jami'an 'yan sanda na musamman da ke kan samun horo, wadanda ake koyar dasu irin aika aikar da zasu yi idan har aka turasu tafka magudin zabe a lokacin da ake kada kuri'u.

"Wannan ne ma babban dalilin da shugaba kasar ya dage lallai sai Sifeta Janar na 'yan sanda ya wuce wa'adin da dokar kasar ta tanadar masa."

Kungiyar ta yi kira ga shugaban kasa Buhari da ya mayar da hankali akan rayuwakan 'yan Nigeria da ake kashewa a Zamfara, Filato, Kudancin Kaduna, Borno da kuma wasu jihohi na kasar, mai makon mayar da hankali kan ganin lallai sai ya yi nasara a zabensa karo na biyu.

SANARWA: Shafin jaridar NAIJ.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa. Muna fatan za ka ci gaba da kasancewa tare da Legit.ng Hausa don karanta labarai da dumi duminsu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Source: Legit.ng News

Tags:
Mailfire view pixel