An gyara makarantu sama da 1, 000 a cikin shekaru 3 a Katsina

An gyara makarantu sama da 1, 000 a cikin shekaru 3 a Katsina

Mun samu labari cewa Gwamnatin jihar Katsina ta gyara makarantu da-dama a cikin shekaru 3 domin inganta harkar ilmi. Gwamna Aminu Bello Masari na jihar ne ya bayyana wannan a wata hira da yayi.

An gyara makarantu sama da 1, 000 a cikin shekaru 3 a Katsina

Masari ya gina dakin karatu fiye da 700 a Makarantun Firamare
Source: Twitter

Mai girma Gwamna Aminu Bello Masari ya bayyana irin yunkurin da gwamnatin APC ta ke yi na dawo da martabar ilmi a jihar Katsina, inda yace kawo yanzu sun gina sababbin dakunan karatu, sannan kuma gyara makarantun jihar.

Rt. Hon. Bello Masari yake cewa daga 2015 zuwa yanzu, sun dauki sababbin malaman makaranta kusan 2000 aiki a jihar Katsina. Daga ciki akwai fiye da mutum 1000 da aka tura makarantun firamare domin ganin an gyara harkar ilmin Boko.

Gwamnan ya kuma bayyana cewa har yanzu ana cigaba da daukar kwararrun malamai aiki a makarantun gwamnati. Duk da wannan yunkuri, gwamnatin jihar ta kuma maida wasu Malamai masu digiri zuwa ma’aikatar ilmi da ke jihar.

KU KARANTA: An garzaya da Dino Melaye zuwa asibitin 'Yan sanda

Aminu Masari, har wa yau, ya tabbatar da cewa gwamnatin sa ta samar da tebura da kujerun karatu fiye da 38, 000. Bayan nan kuma an gina dakunan karatu 13000 saboda karin dalibai. Sai dai duk da haka ana bukatar tebura har kusan 60, 000.

Duk da irin kokarin da gwamnatin Masari tayi na gyara makarantu 1024, har yanzu akwai sauran aiki. Gwamnan yace jihar Katsina ta na bukatar Malamai 16, 000, wanda hakan zai yi wahalar samu saboda matsalar rashin kudi da kwarewa.

Dazu kun ji cewa Gwamna Aminu Masari ya nada wani kwamiti karkashin sakataren gwamnatin jihar wanda zai duba sha’anin tsaro. Gwamnatin Jihar za ta yi kokari wajen maganin satar jama’a da ake yi.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel