Yanzu yanzu: IGP Idris ya yi biris da Dino Melaye a shelkwatar rundunar 'yan sanda

Yanzu yanzu: IGP Idris ya yi biris da Dino Melaye a shelkwatar rundunar 'yan sanda

Rahoton da Legit.ng ke samu daga shafin jaridar Daily Trust, na nuni da cewa, Sifeta Janar na rundunar 'yan sanda, yaki ganawa da Sanata Dino Melaye, a lokacin da ya kai kansa shelkwaar rundunar da ke Abuja. Rahotannin sun bayyana cewa Sifeta ya ki ganawa da Melaye ne, sakamakon wani muhimmin taro da ya shiga.

Sifeta Janar na rundunar 'yan sanda, Ibrahim Idris, ya soke bukatar ganawa da sanata Dino Melaye, wanda ya je shelkwatar rundunar 'yan sandan don ganawa da shugabansu.

Rahotanni sun bayyana cewa, Sanatan, wanda ke wakiltar mazabar Kogi ta Yamma, ya mika kansa ga hukumar 'yan sanda ne a yammacin ranar Juma'a a Abuja.

Wannan ya biyo bayan kusan kwanaki 8 da rundunar ta mamaye gidansa da ke Maitama.

KARANTA WANNAN: Akwai rikici idan APC ta tafka magudi a zaben 2019 - Tsohon gwamnan Niger, Aliyu

Yanzu yanzu: IGP Idris ya yi biris da Dino Melaye a shelkwatar rundunar 'yan sanda

Yanzu yanzu: IGP Idris ya yi biris da Dino Melaye a shelkwatar rundunar 'yan sanda
Source: Twitter

Rahotanni sun bayyana cewa, Melaye ya mika wuya ne ga 'yan sandan, bayan da wasu abokan aikinsa suka shiga tsakani, inda suka bashi kwarin guiwar yin hakan.

Ya je shelkwatar rundunar 'yan sanda ne do ganawa da Insfita Janar na rundunar, sai dai rahotanni sun bayyana cewa bai samu damar ganin Idris ba, kasancewar ya shiga wani muhimmin taro.

Sanatan, wanda ya isa shelkwatar tare da wasu abokan aikinsa, ya zarce kai tsaye ga sashe na musamman da ke aiki kan dakile fashi da makami (SARS).

SANARWA: Shafin jaridar NAIJ.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa. Muna fatan za ka ci gaba da kasancewa tare da Legit.ng Hausa don karanta labarai da dumi duminsu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel