Yanzu Yanzu: ASUU ta amince za ta shiga a dama da ita a zabe

Yanzu Yanzu: ASUU ta amince za ta shiga a dama da ita a zabe

- Kungiyar ASUU ta amince da shiga a dama da ita a zabe mai zuwa

- Sun amince da hakan ne bayan wani ganawa tsakanin hukumar zabe mai zaman kanta (INEC) da jami’an kungiyar a Abuja

Kungiyar malaman jami’a (ASUU) ta amince da shiga a dama da ita a zabe mai zuwa.

An shiga yarjejeniyar ne bayan wani ganawa tsakanin hukumar zabe mai zaman kanta (INEC) da jami’an kungiyar a Abuja.

Yanzu Yanzu: ASUU ta amince za ta shiga a dama da ita a zabe

Yanzu Yanzu: ASUU ta amince za ta shiga a dama da ita a zabe
Source: UGC

Mahmood Yakubu, shugaban INEC, a ranar Alhamis, 4 ga watan Janairu ya tayar da wani batun cewa daga jami’o’i ne abokan aikinsu da dama suke.

Ci gaban na zuwa ne bayan ASUU reshen jami’ar Ibadan sun fada ma INEC cewa kada ta dogara da dalibai da malamai a zabe mai zuwa.

KU KARANTA KUMA: Amina Zakari ba jinin shugaba Buhari bace – Aliyu Abdullahi

A wani lamari na daban mun ji cewa, jam’iyyun siyasa 91 da aka yi wa rijita a karkashin kungiyar Inter-Party Advisory Council sun yi kira ga hukumar zabe mai zaman kanta (INEC) da ta yi gaggawan janye nadin da ta yi wa Amina Zakari a matsayin shugabar kwamitin sanar da sakamakon zabe.

IPAC wata kungiya ce da INEC ta amincewa kuma ta ke magana a madadin dukkanin jam’iyyun siyasa a kasar.

Da yake magana da majiyarmu a ranar Juma’a, shugaban IPAC, Mista Peter Ameh ya nemi INEC da ta cire Zakari domin ganin anyi zabe na gaskiya.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Source: Legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel