Sufeto Janar ya mayar da mukamin Kwamishinan 'Yan sanda na jihar Imo

Sufeto Janar ya mayar da mukamin Kwamishinan 'Yan sanda na jihar Imo

A yayin da a iya kiran lamarin kwan-gaba-kwan-baya, bayan kwanaki biyu kacal, Sufeto Janar na 'yan sanda Ibrahim Idris, ya yi amai ya lashe dangane da sauya wuraren aiki da yiwa kasa hidima na wasu kwamishinonin 'yan sandan Najeriya.

Bayan da 'yan takarar kujerar gwamnan jihar Imo suka huro wuta mun samu cewa, a yau Juma'a sufeto janar na 'yan sanda Ibrahim Idris, ya dawowa da kwamishinan 'yan sanda na jihar Imo, Dasuki Galadanci kan bakin aikin sa.

Wannan lamari ya bayu ne bayan kwanaki biyu kacal da Sufeto Janar ya sauya wuraren aiki na kwamishinan 'yan sanda da kuma wasu manyan jami'an 'yan sandan jihar Imo a yayin sake sabon lale hukumar.

Sufeto Janar ya mayar da mukamin Kwamishinan 'Yan sanda na jihar Imo

Sufeto Janar ya mayar da mukamin Kwamishinan 'Yan sanda na jihar Imo
Source: UGC

'Yan takarar kujerar gwamnan jihar sun yi zargi tare da misalta wannan lamari na sauya wuraren aikin manyan jami'an sandan a matsayin wani yunkuri na kulla tuggu da magudi yayin babban zaben domin ya kasance ni'ima ta alfarma ga jam'iyya mai ci ta APC.

Kazalika akwai Mataimakan kwamshinonin 'yan sanda 3 ma su babban matsayi da kuma Mataimakan kwamishinonin 'yan sanda 11 ma su karamin matsayi da Sufeto ya sauyawa wuraren aiki cikin jihohin kasar nan.

KARANTA KUMA: Zan kammala dukkanin ayyukan da PDP ta watsar a Kudu maso Gabas - Buhari

A ranar Larabar da ta gabata ne IG na kasa, ya nemi kwamishinan 'yan sanda Galandanci, akan ya karkatar da akalar sa ta aiki zuwa jihar Bauchi inda ya kuma dawo da kwamishinan 'yan sanda na jihar Kogi zuwa jihar ta Imo.

Rahotanni sun bayyana cewa, Sufeto janar ya yi wannan kira ne da safiyar yau ta Juma'a, inda ya lashe amansa da cewa, dukkanin manyan jami'an tsaron su koma tsaffin wuraren su na aiki inda suka fi wayo.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da Shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo cikin shafukan mu na zaurukan sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Source: Legit

Mailfire view pixel