Hukumar CAC ta kara wa’adin rage kudin rijistan kasuwanci zuwa 31 ga watan Maris

Hukumar CAC ta kara wa’adin rage kudin rijistan kasuwanci zuwa 31 ga watan Maris

- Hukumar kula da harkokin kasuwanci ta kara wa’adin rage kudin rijistan kasuwanci ga wadanda keda burin yiwa kasuwancinsu rijista

- CAC ta bayyana cewa bayan rage kudin yiwa kasuwanci rijinsta daga N10,000 zuwa N5,000, an kuma kara wa’adin shirin zuwa ranar 31 ga watan Maris

- Tace karin wa’adin ne domin a ba masu kananan sana’o’i damar da za su gabatar da kasuwancinsu ta yadda zai basu damar bude asusun banki, samun damar karbar bashi, da duk wani shiri na gwamnati

Hukumar kula da harkokin kasuwanci, a ranar Alhamis, 3 ga watan Janairu ta kara wa’adin rage kudin rijistan kasuwanci ga wadanda keda burin yiwa kasuwancinsu rijista.

Hukumar CAC ta kara wa’adin rage kudin rijistan kasuwanci zuwa 31 ga watan Maris

Hukumar CAC ta kara wa’adin rage kudin rijistan kasuwanci zuwa 31 ga watan Maris
Source: Facebook

Hukumar ta bayyana cewa bayan rage kudin yiwa kasuwanci rijinsta daga N10,000 zuwa N5,000, an kuma kara wa’adin shirin zuwa ranar 31 ga watan Maris.

Hukumar gwamnatin ta bayar da sanarwar ne a shafinta na twitter, @cacnigeria1.

KU KARANTA KUMA: Jam’iyyu 91 sun nemi INEC ta tsige Amina Zakari a matsayin shugabar kwamitin zabe

Hukumar ta kara da cewa Karin wa’adin ne domin a ba masu kananan sana’o’i damar da za su gabatar da kasuwancinsu ta yadda zai basu damar bude asusun banki, samun damar karbar bashi, da duk wani shiri na gwamnati.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Source: Legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel