Sojoji sun ragargaji 'yan ta'adda a wasu kauyukan Borno, sun kashe guda shida

Sojoji sun ragargaji 'yan ta'adda a wasu kauyukan Borno, sun kashe guda shida

- Dakarun Sojin Najeriya da Civilian JTF sunyi nasarar lalata mafakan 'yan ta'adda a kauyukan Borno

- Dakarun sojin sun halaka 'yan ta'adda guda shida a yayin da suka yi dirar mikiya a mafakan na 'yan ta'addan

- Sun kuma yi nasarar ceto mata guda uku tare da kwato makamai da alburusai da bindigu kafin su lalata mabuyar 'yan ta'addan

A jiya Alhamis ne dakarun sojin Najeriya na 22 Brigade masu atisayen Operation Lafiya Dole tare da wasu 'yan kato da gora da akafi 'Civilian JTF' suka kai sumame a wasu mafakan mayakan Boko Haram a kauyukan Gawa da Boskoro da ke karamar hukumar Mafa na jihar Borno.

Sanarwar da ta fito daga bakin mai magana da yawun soji, Brig. Janar Sani Usman ya ce a dakarun sojojin sunyi nasarar gano mafakan mayakan Boko Haram tare da lalatasu kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

Dakarun Soji sun fattaki 'yan Boko Haram daga wasu kauyukan Borno

Dakarun Soji sun fattaki 'yan Boko Haram daga wasu kauyukan Borno
Source: Facebook

DUBA WANNAN: Dalilin da yasa Buhari ya kaddamar da yakin neman zabensa a Akwa Ibom - Masari

Ya kara da cewa "sunyi nasarar kawar da 'yan ta'adda shida a garin. A yayin da suke bincike kafin kone wurin, sojin sun gano bindigu 4, gurnetin hannu guda 3 da harasai da yawa."

Ya kuma ce sun gano tukunyoyin iskar gas guda uku da kwari da baka.

Ya ce tawagar sojojin sun kuma ceto mata guda uku a Boskoro inda daga bisani aka mika su hannun masu kula da sansanin 'yan gudun hijira da ke Dikwa.

Usman ya ce kwamandan Lafiya Dole, Manjo Janar BA Akinroluyo ya gamsu da namijin kokarin da su kayi hakan yasa ya yada musu.

Ya kuma umurci su cigaba da nuna jarumta da kwarewa wurin binciko dukkan inda 'yan ta'addan ke buya domin ganin an kawo karshen wannan fitinar.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel