Dalilin da ya sa muka kai mamaya gidan jaridar Daily Trust – Sojoji

Dalilin da ya sa muka kai mamaya gidan jaridar Daily Trust – Sojoji

- Rundunar sojin Najeriya ta ce ta kai mamaya gidan jaridar Daily Trust a Maiduguri da Abuja

- Sun kai mamayar ne don gayyatan yan jaridar kamfanin da suka buga labarin wani shirye-shirye na sojojin

- Usman yayi bayanin cewa bayyana irin wannan bayani da jaridar tayi barazana ne ga tsaron kasa don haaka aka gayyaci masu kawo rahoton don amsa tambayoyi

Rundunar sojin Najeriya ta ce ta kai mamaya gidan jaridar Daily Trust a Maiduguri da Abuja, domin gayyatan yan jaridar kamfanin da suka buga labarin wani shirye-shirye na sojojin.

Rundunar sojin ta yarda da kai mamaya gidan jaridar a wani jawabi daga kakakinta, Birgejiya Janar Sani Usman.

Usman yayi bayanin cewa bayyana irin wannan bayani da jaridar tayi barazana ne ga tsaron kasa don haaka aka gayyaci masu kawo rahoton don amsa tambayoyi.

A cewarsa, anyi gayyatan ne domin ci gaba da bincike, sannan kuma idan bukata ta taso, dukkanin wadanda aka kama da barazana ga tsaro za su fuskanci hukunci daidai da wanda dokar hukumar ta tanada.

Dalilin da ya sa muka kai mamaya gidan jaridar Daily Trust – Sojoji

Dalilin da ya sa muka kai mamaya gidan jaridar Daily Trust – Sojoji
Source: Depositphotos

Sojoji tare da yan sanda sun kai mamaya ofishgin a ranar Lahadi kan wani labara, da yayi bayanin wani babba aiki da sojojin ke shirin gudanarwa domin kakkabe Boko Haram daga Baga da kewayenta.

Gamayyar kungiyar na Al-Banarwi ta kai hari iyakar garin da kewaye jim kadan bayan bikin Kirsimeti.

Baga ya kasance gari a yankin arewacin Borno.

KU KARANTA KUMA: Rundunar Sojojin Gabon sun yi wa Shugaba Ali Bango juyin mulki

Ya ci gaba da bayanin cewa an yi gayyatar ne da kyakyawan kudiri domin bari masu kawo rahoto su gane muhimmancin irin haka ga tsaron kasa.

Kakakin sojojin ya bukaci yan jarida da kada su damu da matakin “cewa su ci gaba da ayyukan gabansu na kawo rahoto sannan su nuna kwarewa kamar yadda hukumar sojin bata da niyan tauye hakkin yan jarida.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Source: Legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel