Yadda Dino Melaye ya kai kansa zuwa ga Sufeto Janar na 'Yan sanda

Yadda Dino Melaye ya kai kansa zuwa ga Sufeto Janar na 'Yan sanda

Bayan kwanaki takwas na kwayanya da sintiri da jami'an 'yan sanda su ka zage su na aiwatarwa a harabar gidan Sanatan shiyyar Kogi ta Yamma, Sanata Dino Melaye, a yau Juma'a ya kama hanyar sa ta zuwa hedikwatar jami'an tsaro domin ganawa da sufeto janar na 'yan sanda Ibrahim Idris.

Rahotanni kamar yadda jaridar The Punch ta ruwaito, Sanata Melaye ya sulale cikin tawagar Sanatoci da suka ziyarci gidan sa da ke unguwar Maitama a yau Juma'a, inda zuka garzaya zuwa ga babban jagoran na 'yan sanda domin neman sulhu tsakanin sa da hukuma.

Hukumar 'yan sandan Najeriya na ci gaba da zargin Sanata na jihar Kwara da babban laifin na ta'addanci, inda wasu yan gani kashenin 'yan barandasa suka raunata wani raunata wani jami'in dan sanada tun a watan Yulin shekarar da ta gabata.

Yadda Dino Melaye ya kai kansa zuwa ga Sufeto Janar na 'Yan sanda

Yadda Dino Melaye ya kai kansa zuwa ga Sufeto Janar na 'Yan sanda
Source: Twitter

Majiyar jaridar Legit.ng ta ruwaito cewa, a halin yanzu wannan jami'in dan sanda da ya sha harbi na bindiga, Sajen Aliyu, na ci gaba da samun kyakkyawar kulawa a gadon asibiti na babbar cibiyar lafiya da ke birnin Lokoja na jihar Kwara.

Kimanin jami'an 'yan sanda 50 ne suke yiwa harabar gidan Sanatan kawanya tun a makon da ya gabace mu tare da girki wata na'ura mai toshe duk wata kafar sadarwa, sai dai gogan ya mai she da lamarin tamkar bai san suna yi ba.

KARANTA KUMA: Harin Buni Gari: An sake tsinto gawar sojoji 3 cikin dokar Daji a Yobe

Sanata Dino ya aike da sakonni a shafin sa na zauren sada zumunta na Twitter, inda ya rika cewa ba zai saduda ba domin kuwa yana zargin 'yan sandan za su yi ma sa allurar mutuwa ne, ko da yake 'yan sandan sun musanta zargin.

Binciken manema labarai ya tabbatar da cewa, Sanata Melaye ya garzaya ofishin hukumar 'yan sanda na musamman masu yakar fashi da makami watau SARS, inda zai amsa tambayoyi yayin da hakar sa ba ta cimma ruwa ba wajen neman ganawa da babban Sufeton na 'yan sanda.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da Shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo cikin shafukan mu na zaurukan sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Source: Legit

Mailfire view pixel