Aiki ga mai kareka: IG Ibrahim Idris ya tura sabbin Yansanda dubu biyu jahar Borno

Aiki ga mai kareka: IG Ibrahim Idris ya tura sabbin Yansanda dubu biyu jahar Borno

A kokarin gwamnatin Najeriya na kakkabe ragowar mayakan kungiyar ta’addanci na Boko Haram da suka addabi jihohin Borno da Yobe a yankin Arewa maso gabas, babban sufetan Yansandan Najeriya, IG Ibrahim Idris ya aika da sabbin Yansanda guda dubi biyu zuwa Borno.

Babban kwamandan yaki da Boko Haram a filin daga, Manjo Janar Benson Akinruloyu ne ya sanar da haka a ranar Juma’a 4 ga watan Janairu yayin da yake gabatar da jawabin maraba ga Yansandan a sansanin Sojojin Atilari na 333 dake Maiduguri.

KU KARANTA: https://hausa.legit.ng/1213358-handama-da-babakere-attahiru-bafarawa-ya-shigar-da-karar-alu-wammako-gaban-efcc.html

A jawabin nasa, Kwamanda Benson ya nemi dasu kasance masu taka tsantsan wajen gudanar da aikinsu, nuna kwarewa a bakin aiki tare da kula da hakkin bil adama, da kuma dokokin kasa, kamar yadda majiyar Legit.com ta ruwaito.

“Shelkwatan tsaro da kuma babban shelkwatar yaki da ta’addanci ta Operation Lafiya Dole na da kyakkyawan zato akanku, don haka muna fatan ba zaku bamu kunya ba, ina tabbatar muku cewa ba zan lamunci cin zarafin dan adam ba ko wani iri.

“Don haka wajibi ne a gareku ku kasance kun shaku da jama’an garuruwan da zaku kare ba tare da kun kaskantar da aikinku ko mutuncinku ba, kamar yadda ake yayatawa cewa Dansanda abokin kowa ne.” Inji Kwamanda Benson.

Bugu da kari kwamandan ya kara da cewa an tura Yansandan ne domin rikewa tare da kula da tsaron garuruwan da Sojoji suka kwace daga hannun mayakan Boko Haram suka fatattakesu, kuma a cewarsa Yansandan sun samu horon data dace.

Ya tabbatar da cewa an tanadi kayan barci, kayan aiki da kuma alawus alawus dinsu don ganin sun gudanar da aikinsu cikin kwanciyar hankali, ya kara da cewa zasu tura Yansandan zuwa Bama, Gubio, Dikwa, Damboa da Maiduguri.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel