Zaben 2019: INEC ta kafa kwamiti don ganawa da ASUU, NLC

Zaben 2019: INEC ta kafa kwamiti don ganawa da ASUU, NLC

- Hukumar INEC, ta kafa wasu kwamitoci guda biyu, don tabbatar da kammaluwar shirye shiryen zaben 2019, ba tare da an samu wata tangarda ba

- INEC ta ce tana iya bakin kokarinta na ganin cewa yajin aikin da ASUU bai shafi aikin zaben ba

- Haka zalika, INEC ta bayyana cewa ta shirya gudanar da wani taron ganawa da kungiyar kwadago ta kasa NLC da NURTW a mako mai zuwa

Domin tabbatar da cimma shirye shiryen babban zaben 2019, hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa INEC, ta kafa wasu kwamitoci guda biyu, don tabbatar da kammaluwar shirye shiryen zaben 2019, ba tare da an samu wata tangarda ba.

A cewar shugaban hukumar INEC, Farfesa Mahmood Yakubu, wanda ya sanar da hakan a wani taron manema labarai a shelkwatar hukumar da ke Abuja, a ranar 3 ga watan Janairu, kwamitin farko zai kula da alhakin duk wasu tsare tsare na zaben.

KARANTA WANNAN: Yanzu yanzu: Kwastam ta damke motar Dangote dauke da haramtacciyar shinkafa

Zaben 2019: INEC ta kafa kwamiti don ganawa da ASUU, NLC

Zaben 2019: INEC ta kafa kwamiti don ganawa da ASUU, NLC
Source: Depositphotos

Farfesa Mahmood Yakubu ya kuma bayyana cewa, hukumar ta gana da shuwagabannin kungiyar malaman jami'o'i ta kasa ASUU a ranar Juma'a a Abuja, da misalin karfe 4 na yamma, don tattauna batutuwan da suka shafin yajin aikin da kungiyar ke kanyi, tare da samun mafita kan amfani da malamai da dalibai a aikin zaben 2019.

Shugaban hukumar ya ce: "Mun damu kwarai, kasancewar kaso mai tsoka na ma'aikatan zabe ana zakulo su daga jami'o'i. Muna iya bakin kokarinmu na ganin cewa yajin aikin da ASUU ke yi bai shafi aikin zaben ba. ASUU a daga cikin manyan masu ruwa da tsaki wajen taimakawa INEC gudanar da sahihin zabe."

Haka zalika, Yakubu ya bayyana cewa hukumar ta shirya gudanar da wani taron ganawa da kungiyar kwadago ta kasa NLC a mako mai zuwa, inda yake cewa: "Muna a shirye muyi aiki kafada-da-kafada da kungiyar NLC, NURTW, kamar yadda muka kulla yarjejeniya (MoU), kan kayan aiki da kuma ma'aikatan da zasu bamu don gudanar da zabe mai zuwa."

SANARWA: Shafin jaridar NAIJ.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa. Muna fatan za ka ci gaba da kasancewa tare da Legit.ng Hausa don karanta labarai da dumi duminsu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Source: Legit Nigeria

Tags:
Mailfire view pixel